MUNFISO MUYI SULHU DA KORIYA INJI KASAR AMURKA
……idan Kuma Ta Kama Zamu Kai Mata Hari Inji Doland Trump
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump yace idan ta kama sai ya kai wa Koriya ta Arewa hari don ya taka masu burki wajen makami mai linzamin da su ke harbawa.
Makami mai linzamin Kasar Koriya ta Arewa Kwanan nan Kasar Koriya ta Arewa ta saki wani mugun makami mai linzami wanda ka iya dura kan Garin Alaska.
Amurka tace dole a takawa Koriya burki ko ta karfi da yaji idan ta kama don ta saba doka bayan da ta saki wani mahaukacin makami mai linzami.
Irin makaman da Kasar Koriya ta Arewa ta ke saki Amurka tace za ta fi so a zauna yi sulhu amma fa idan abin ya faskara dole Kasar ta tashi tsaye.
Kwanan nan dai Koriya ta saki makamin nukiliya da zai iya ratsawa har Kasar Amurka wanda Donald Trump yace ba zai yarda hakan ta faru ba.
Ya kuke Ganin wannan Fada Na Amurka Da Koriya?
Add Comment