Labarai

Muna tare da Japan kan gwajin makami mai linzami — Trump

Korea ta Arewa ta yi gwaje-gwajen makamai masu linzami da dama a baya
Korea ta Arewa ta harba wani makami mai linzami a wani gwajin farko tun hawan mulkin shugaban Amurka, Donald Trump.
Mista Trump ya tabbatar wa Firai ministan Japan, Shinzo Abe cewa “Amurka tana tare da Japan kan al’amarin, dari bisa dari.
Makamin mai linzami dai ya yi tafiyar nisan mil 300 a inda ya nufi tekun da ke Japan, sai dai kuma jami’an kasar sun ce makamin bai kai ga tekun kasar. 
Mista Abe ya ce gwajin “abin da za a zura ido a kalle shi ba ne”
Da yake magana yayin wani taron ‘yan jaridu na hadin gwiwa lokacin ziyararsa a Amurka, Mista Abe ya kara da cewa mista Trump ya ba shi tabbacin “kara karfin dangantaka da kawance tsakanin kasashen biyu.”
A lokacin yakin neman zabensa dai, Donald Trump, ya ce, irin yadda Amurka take mayar da hankalinta ga tsaron kasashen Japan da Korea ta Kudu, ya wuce kima, a inda ya nemi kasashen da su dauki nauyin zaman sojojin na Amurka a yankunansu.
Mista Trump ya ce gwajin makami mai linzami barazana ceHakkin mallakar hotoAP
Image captionDonald Trump ya ce Amurka na tare da Japan dari bisa dari
Kasar Korea ta Arewa dai da gudanar da gwaje-gwajen makamai masu linzami da dama a shekarun da suka gabata, al’amarin da ke barazana ga sauran kasashen yankin.
Gwajin makamin na ranar Asabar daga sansanin da ke Banghyon a arewacin lardin Pyongan na yammacin kasar ta Korea ta Arewa.
An dai ce makamin yana da dogon zango.
Da man dai a watan Janairu, shugaban Korea ta Kudu, Kim Jong-un ya ce kasarsa za ta yi gwajin wani makami mai linzami mai dogon zango wanda yake da karfin tankarar da Amurka.
Sai dai kuma shugaban Amurka, Donald Trump ya karyata batun, a wani sakon da ya wallafa ta shafinsa na Twitter, yana mai cewa “Hakan ba abu ne mai yiwuwa ba.”
Japan dai na ganin gwajin barazana ce gare taHakkin mallakar hotoREUTERS
Image captionIiren gwaje-gwajen makami mai linzami da Korea ta Arewa ta yi
Yanzu dai haka Japan, ta ce za ta mayar da martani kan wannan al’amari.
To amma har kawo yanzu Korea ta Arewa ba ta ce uffan ba tun bayan gwajin makamin da ta yi.
Yayin wata ziyara kasar, a makon da ya gabata, Sakataren tsaron Amurka, James Mattis, ya ce duk wani yunkurin yin amfani da makamin nikiliya da Koriya ta Arewa ke yi, zai “fuskanci martani dai-dai gwargwado.”
Sannan ya kara bayar da tabbacin kai injina masu kare kasa daga makami mai linzami mallakar Amurka zuwa Japan domin ita ma ta kare kanta, nan gaba a cikin wannan shekarar.
Shi ma Ministan harkokin waje na Korea ta Kudu, ya ce “ci gaba da tsokanar da gwamnatin Kim Jong-un ke yi, na nuni da irin wautar kasar na tunanin mallakar makamin nukiliya.”
A shekarar 2016 kadai, Koriya ta Arewa ta gudanar da gwaje-gwajen makamai masu linzami har guda biyar.
Ta kuma yi ikrarin cewa za ta iya kai wa Amurka hari irin na makamin nukiliya.
Sai dai kuma har kawo yanzu, masana makami mai linzami suna kokwanton kera makamin da zai iya kai wa ga Amurka saboda a cewarsu har yanzu da sauran Koriyar ta Arewar.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.