A Jamhuriyar Nijar wasu masana na fafutikar ganin an fassara kundin tsarin mulkin kasar ya zuwa harsunan gida.
Harsunan farko da masanan za su aiki kai su ne Hausa, zabarmanci da kuma Barbarci.
A ayarsa ta 43, kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar din ya tanadi cewa hukumomin kasar su tabbatar da cewa ana koyar da dokokin tsarin mulkin a makarantun bokon kasar, tare da fadakar da al’umma game da abinda ya kunsa.
Hakan ne dai ya sa aka rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin wata cibiya ta ‘yan jaridu da ke kula da yada labarai cikin harsunan gida , da kuma kungiyar masana tsarin mulki ta Nijar, don gudanar da ayyukansu kafada da kafada.
Daga ciki akwai aikin fassarar kundin tsarin mulki na kasar cikin harsuna uku, wato Hausa, da Zabarmaci da kuma Barbarci.
A wata hira da BBC , sakataren kungiyar masana tsarin mulkin Maina Bukar, ya ce muhimmancin fassarar kundin tsarin mulkin kasar zuwa wadannan harsuna zai sa ‘yan kasar su samu damar karanta duk wata doka da ta shafi ci gaban kasa, da dimokradiyya, da sauransu.
” Idan akwai harsuna kamar Hausa, da Zabarmacin da Barbarci, wadanda yawanci ‘yan Nijar na amfani da su, don haka zai kara bai wa yare namu na Nijar daraja”, in ji Maina Bukar.
Ya kuma ce da hakan ne zai sa harsunan gida za su bunkasa, tare da kare su daga barazanar bacewa.
Masanin dai ya ce kundin tsarin mulkin ya tanadi cewa duka harsunan kasar darajarsu daya ce, don haka duka kasa tana iya amfani da su.
Souce In Bbchausa
Add Comment