Labarai

Muna Nan Zuwa Kanku, Sakon Shugaban Sojojin Nijeriya Ga Igboho Da Dokubo

Daga Abubakar A Adam babankyauta
Shugaban rundunar sojojin Nijeriya, Laftanal Janar Attahiru ya ce suna nan zuwa kan Sunday Igboho da Asari Dokubo.

Babban hafsin sojan ya ce babu shakka za su yi iyakar kokarinsu wurin ganin sun tabbatar da sun fatattaki duk wani nau’in rashin tsaro

Janar Attahiru ya sha alwashin ganin bayan duk wasu masu tada kayar baya ko kungiyoyin assasa rashin tsaro.

Rundunar sojin Nijeriya nan kusa za ta koma farautar masu tada kayar baya kamar su Sunday Igboho da Asari Dokubo, a cewar Laftanal Janar Ibrahim Attahiru yace.

Jan kunnan babban hafsan yana zuwa ne a daidai lokacin da ya halarci taron horar da kwamandojin soja na 2021.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, a cikin kwanakin nan ne Igboho ya bayyana cewa yankin kudu maso yamma baya daga cikin Nijeriya.

Dokubo ya sanar da samar da gwamnatin gargajiya ta Biafra wacce ta hada da wasu sassan kudu maso gabas da kudu kudun kasar nan.

Amma Attahiru yayi alkawarin cewa zai maganin duk wani kalubalen tsaro da ke addabar kasar nan, wanda ya hada da masu tada kayar baya irinsu Igboho da Dokubo.

Muna rokon Allah ya daura dakarun sojojin Nijeriya akan ‘yan ta’addan Nijeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: