Muna da Hannu wajan rashin Aikin yi a Jahar Kano- Inji Alh. Aliko Dangote


0 190

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A wajan wani taro a jami’ar Bayero da kungiyar (Kano Concerned citizens Initiative) suka shirya Alhaji Aliko Dangote lokacin da yake jawabi akan arzikin jihar Kano da kuma girman kasuwar Kano, ya bayyana cewa ba za su bar Mai martaba Sarki Malam Muhammadu Sanusi ll shi daya ba wajen fadar gaskiya har a dinga ganin ya matsa da yawa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Attajirin ya kara da cewar suma yanzu lokaci ya yi da za su dinga fadar gaskiya, ya ce “gaskiya ne su ne za su bawa mutane aiki amman sai gwamnati ta bada damar hakan wajen buda hanyar da za su kafa masana’antu a jihar Kano don al’ummar jihar Kano su samu aiki.

Ya ce lokaci ya yi da za’a raya masana’antun jihar Kano da suka mutu ko aka rufe a dalilin rashin wutar lantarki. Amma mun shirya tsaf domin taimakawa yaranmu da suke yawo a titi, zamu zauna mu duba biliyoyin da zamu zuba ni da Abdussamad don samar da ci gaban jiharmu ta Kano.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.