-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Mun Yi Nadamar Zaben Buhari, Cewar Kungiyar Matasan Arewa


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai da suka kira, Shugaban Kungiyar ta Matasan Arewa Alhaji Shettima Yerima, yace ya zama wajibi a garesu a matsayin su na Shugabannin Matasa a Arewa, su nuna damuwa da bakin cikin su akan abinda ya kira zaben tumun Dare da suka yi kuma suka sa Matasan Arewa su kayi ta hanyar zaben Buhari wanda suka bayyana a matsayin mara kishin Arewa.

Shugaban Matasan Arewan ya kara da cewar, ko kadan Buhari bai dace da shugabancin Nijeriya ba, domin a fili yake Babbar Kasa irin Najeriya ta fi karfin Mutum irin Buhari, wanda bai da gogewa ta bangaren ilimi, ko harkokin kasuwanci, hakan ya sa kullum Arewa sai kara fuskantar koma baya take, Talauci na cigaba da kisan kare Dangi ga Jama’ar yankin, amma abin mamaki Buhari ko a Jikinshi, sai cigaba da kwarabniya yake, ya zama Misalin makahon direba ya kwashi Jama’a zai kai ga halaka.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 660

- Advertisement -

Alhaji Yerima ya cigaba da cewar ya zama wajibi ayi taron Dangi a kawar da Buhari daga mulki a 2019 kafin ya karasa kassara yankin Arewa, inda yace wannan shine babban dalilin da yasa sanannen Dattijon nan mai kishin Arewa Farfesa Ango Abdullahi ya fito fili ya ankarar da Jama’a hatsarin cigaba da mulkin Buhari, saboda babu abinda Buhari yayi na cigaba a Arewa, dukkanin ayyukan raya kasa an tattara su gaba daya a Jihohin Yarbawa, saboda Manyan Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya uku a dauka an damkawa Mutum guda Bayarabe Fashola, wato Ma’aikatun Ayyuka da haske Wutar Lantarki da Gidaje, shin babu Dan Arewan da ya Cancanta ne wanda za’a dauki daya daga cikin Ma’aikatun nan a bashi ne? Amma maimakon a fahimci maganar Ango Abdullahi sai aka fito ana ta zagin shi.

Shugaban Matasan Arewan ya bayyana cewar, Allah yayi wa ‘Yan Arewa ilhama, tun da Buhari da kanshi ya fito yace tattalin Arzikin Najeriya ya karye, wato abinda hakan ke nufi shine ‘yan Najeriya musanman’yan Arewa zasu kara shiga cikin wata rayuwa mai kunci fiye da wacce suke ciki a yanzu, kuma tuni matarshi

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: