Rundunar sojin Najeriya ta bayyana alhininta game da harin da kungiyar Boko Haram ta kai wanda ya zama saniyyar mutuwar ma’aikatan da ke binciken mai a gundumar Borno Yesu ta karamar hukumar Magumeri dake jihar Borno.
Ma’aikatan da suka rasa rayukansu sun hada da ma’aikatan kamfanin mai na kasa, NNPC, da wasu ma’aikatan jami’ar Maidugui har da da sojojin da ke raka su tare da ‘yan kato da gora.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin Najeriya, Birgediya-Janar Sani Kukasheka Usman ya sanya wa hannu, rundunar sojojin ta ce abin takaici ne yadda suka sanar da al’umomin Najeriya cewa sun riga sun ceto dukkan ma’aikatan kamfanin NNPC, inda sanarwar ta kara da cewa ba da gangar a ka yi haka ba.
“Kawo yanzu, masu bincike sun gano karin gawarwakin wasu sojoji 5, da ‘yan kato da gora 11 da na jami’ai masu binciken guda 5, kuma ta ce ba a ji duriyar mutum shida cikin ma’aikata goma sha biyun da suka suka fita aikin binciken ba, amma ma’aikacin kamfanin NNPC daya ya tsira da ransa”, in ji sanarwar.
Sanarwa ta kuma bayyana wasu kayan yaki da rundunar sojin da ke yaki da kungiyar Boko Haram ta kwato a hannun kungiyar ta Boko Haram. Kayan sun hada da bindigogi, da motoci, da bama-bamai har da kayan bincike na GPS.
Sanarwar ta cigaba da cewa rundunar sojojin na cigaba da neman inda aka tafi da sauran ma’aikata masu bincike. Ta kuma nuna farin cikinta da irin goyon bayan da take samu daga ilahirin jama’ar yankin.
Add Comment