-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Mun Samu Fahimtar Juna Tsakanin Mu Da Kungiyar Izala -Dr Muhammad Suleiman


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Mun Samu Fahimtar Juna Tsakanin Mu Da Kungiyar Izala – Dr Muhammad Suleiman

Babban Limamin Masallachin Juma’a na Sultan Bello Kaduna Dr Muhammad Suleiman, ya bayyana cewar sun samu fahimtar juna a tsakanin su da bangaren Kungiyar Izala dangane da wa’azin da Kungiyar take gabartawa a Masallachin.

A zantawar da yayi da wakilinmu a Ofishin shi dake Masallachin, Limamin ya cigaba da cewar da fari babu wanda ya tuntube su akan maganar gudanar da wa’azin, sai dai kawai sun samu labarin ne ta kafafen yada labarai, wannan ya sanya Hukumar Masallachin ta kira zaman gaggawa da ‘yan kwamitin ta, daga karshe suka yanke shawarar hana gudanar da taron, bayan sun fitar da sanarwar ne Shugaban Izala na kasa Sheikh Bala Lau ya kira su inda ya nuna damuwa akan yadda masu shirya taron basu tuntube su a karkashin Jagorancin Shugaban Kungiyar na jihar Kaduna Malam Tukur Isa, sannan ya bada hakuri akan kuskuren da akayi.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 660

- Advertisement -

Dr Suleman yace bisa ga wannan suka samu fahimta sosai har wa’azi ya cigaba da gudana, ya kuma shawarci Malamai masu gabatar da wa’azin da su kauce da shiga cikin Hurumin siyasa, ‘yan siyasa na kama da kuli-kuli ne wadanda ba’a san gaban su da bayan su ba, kuma Munbarin Masallachin Sultan Bello na da’awa ne ba na Siyasa ba saboda haka a kiyaye.

Malamin ya kuma yi kira ga Iyaye da su kara sanya idanuwa akan ‘ya’yan su musanman a lokutan zabe dake karatowa, domin Kaucewa shiga rudani mara amfani.

Mikiya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: