Mun Samarwa Mutane Miliyan 12 Aikin Yi, A Bangaren Aikin Noman Shinkafa ~ Cewar Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta samarwa da yan kasar mutane miliyan 12 aikin yi a bangaren noman shinkafa.
Mai magana da yawun shugaban kasa malam Garba shehu shi ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi shii da gidan talabajin na chennel.
Ya ce Buhari ya samar da aikin yi a bangaren noma, wutar lantarki da tsaro a Najariya.
Ya ci gaba da cewa akalla yanzu haka mutane miliyam 12 ne aka samarwa aikin noman shinkafa.
Sannan yanzu kasa Najeriya ta dogara da kanta ne a bangaren kayan masarufi bata bukatar shigo da shi daga wani guri.
Ya ce a lokutan baya kasa Najeriya ta na kashe akalla biliyan biyar domin shigo da kayan abinci, amma yanzu bata kashe ko sisi don wannan.
Kuma gwamnatin shugaba buhari ta gaji kamfanin samar da taki zamani hudu ne amma yanzu akwai 52 a kasar.
Add Comment