Rundunar sojin Nijeriya ta karyata jita-jitar da ke cewa rundunar ba ta kwaso gawarwakin dakarunta da ‘yan ta’addar kungiyar Boko Haram suka yi kwanton bauna ba, a wasu sansanoni uku dake garin Metele na jihar Barno.
Rundunar ta shaida hakan ta shafin ta na Tuwita, wato @HQNigerianArmy, bayan da jita-jita ta cika shafukkan sadarwa, cewa hukumar ta bar gawarwakin dakarunta a yashe a kasa a garin Metele, cikin wanda suka rasa ransu harda ‘yan sa kai wadanda ake ce ma civilian JTF.
Rundunar ba a shafin Tuwita kadai ta sanya wannan maganar ba, har a shafin sada zumuntan ta na Facebook ta sanya, rundunar ta ce ta na samun rahoton harin ta aike da karin dakaru, wadanda suka je musamman don gano gawarwakin dakarun da kuma kwaso gawarwakin, sam ba a bar wata gawa ba a wajen harin.
- Advertisement -
Sannan rundunar ta na kan aikin debo dakarun da suka samu raunuka, su ma ko mutum daya ba a bari ba, rundunar ta koka da yadda wasu shafukkan watsa labarai suke yada labaran karya game da batun wannan harin na Metele, sannan rundunar ta bukaci a dinga tuntubarta don samun labarai na gaskiya ba na karya ba.
#Leadershipayau