Mun Jima Da Karya Lagon Boko Haram, Hare-haren Da Ake Kai Wa A Yanzu

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Mun Jima Da Karya Lagon Boko Haram, Hare-haren Da Ake Kai Wa A Yanzu ‘Yan Kungiyar ISIS Ne, Cewar Janar Buratai

Shugaban sojojin Nijeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya tabbatar da cewa dakarun sojojin Nijeriya sun karya lagon asalin ‘yan kungiyar Boko Haram.

Talla

Abinda yake faruwa yanzu na dukkan hare-haren ta’addanci da ake kaddamarwa akan dakarun sojin Nijeriya da suke yaki a arewa maso gabashin Nijeriya aikin kungiyar ISIS na duniya ne ta reshenta dake kula da yammacin afirka “Islamic State West Africa Province” (ISWAP) karkashin jagorancin Habib Ibn Muhammad Yusuf Abu Mus’ab Al-barnawiy.

Janar Buratai ya kara da cewa wadannan ‘yan ta’addan sun zo da sabon salo ta yadda suka karfafa yada farfaganda ta kafofin watsa labarai domin su sanyaya gwiwar dakarun sojojinmu, amma tabbas abinda ya tabbata shine mun karya lagon ‘kungiyar Boko Haram, yanzu muna yaki ne da wakilcin kungiyar ta’addanci na duniya wato ISIS, a cewarsa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Wannan gaskiya ne, kusan watanni biyu da suka gabaya nayi rubutu akan wannan maganar da yanzu shugaban sojojin Nigeria ya tabbatar, kuma abinda ya kamata kowa ya fahimta kenan, kuma wadannan reshen ‘yan ta’addan zaiyi wahala a samu nasara a kansu matukar kasashen dake kan iyaka da tabkin chadi basu baiwa gwamnatin Nigeria cikakken hadin kai ba

Muna fatan Allah Ya taimaki masu ikon tsaron Nigeria Ya fahimtar dasu hanya mai sauki da za su bi su magance mana dukkan matsalolin tsaro a Nijeriya.

Daga Datti Assalafiy

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: