Mun Gano Mutanen Dake Daukar Nauyin Ta’addanci A Nijeriya, Cewar Ministan Shari’a Abubakar Malami

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Abubakar A Adam babankyauta.
Ministan shari’a Abubakar Malami ya ce binciken da suka gudanar ya nuna musu wasu fitattun ‘yan Nijeriya da kuma ‘yan kasuwar da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a cikin kasar.

Ministan ya ce tuni aka fara shirin gurfanar da wadannan mutane a gaban kotu domin fuskantar shari’a akan rawar da su ke takawa wajen haifar da tashin hankali sakamakon binciken da gwamnati ta gudanar a Daular Larabawa dangane da masu daukar nauyin bai wa boko haram kudade.

Wannan matakin na gwamnati na zuwa ne a dai dai lokacin da kasar ke fuskantar karuwar hare haren ayyukan ta’addanci na boko haram a yankin arewa maso gabas da kuma wasu hare haren na daban a wasu yankuna kasar.

Malami ya ce gwamnati ta dauki dogon lokaci ta na gudanar da bincike akan wannan lamarin da ya shafi ayyukan ta’addanci bayan da kotu a Daular Larabawa ta daure wasu ‘yan Nijeriyar guda shida.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 773

Ministan ya ce binciken da suka dauki dogon lokaci su na yi ya nuna musu wasu mutane da hukumomi da ke da hannu wajen jefa kasar cikin tashin hankali.

Malami ya ce suna da kwararan shaidun da ke nuna musu irin wadannan mutanen da ke daukar nauyin baiwa ‘yan ta’adda kudade kuma yanzu kotu ce za ta tabbatar da wannan zargi.

Saidai mu kuma muna rokon Allah ya tarwatsa gungun yan ta’addan Nijeriya da masu daukar nauyinsu.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: