Mun Gamsu Da Sharhin Da Aka Rika Yi Wa Zaben 2019 -Shugaban INEC


0 143

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Wakilinmu

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce Hukumar Zabe ta gamsu da sharhi da tsokacin da aka rika yi bayan am kammala zabukan 2019.

Sai dai kuma duk da haka, ya ce ba a rasa damuwa ba a wasu ‘yan wurare.

Yakubu ya yi wannan kalamin ne a wurin Taron Yin Tsokaci Kan Zaben 2019, wanda Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Kasa (NUJ), ta shirya a Abuja.

Kwamishinan INEC Na Kasa, Mohammed Haruna ne ya wakilci Shugaban Hukumar Zabe a wurin taron.

Ya ce tun bayan kammala zaben 2019, kungiyoyi daban-daban, na cikin Najeriya da na kasashen waje na ta gudanar da tarukan tattauna yadda zaben ya gudana.

“Duk da cewa a duk inda aka yi taron yin tsokacin ana yaba wa INEC, amma sau da yawa kuma ana sukar wasu abubuwan da suka rika gudana a lokacin zabe, musamman, sayen kuri’u, rikice-rikice da kuma rashin fitowar jama’a su jefa kuri’.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Yakubu ya ce ya na fatan kafafen yada labarai za su fito karara su shaida wa duniya da INEC inda aka samu nasara da kuma inda aka samu cikas.

Sai ya tunatar da cewa a cikin jam’iyyun siyasa 91 da suka shiga zabe, 75 sun yi irin wannan taron, inda suka nuna gamsuwa da yadda INEC ta gudanar da zanen 2019.

“Ina fatan duk abin da NUJ za ta fitar a wannan taron, to ta bayyana su tare da kawo hujjoji na alkaluma da na shaidun zahiri.” Inji Farfesa Yakubu.

Kakakin Yada Labarai na Shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya jinjina wa ‘yan jarida dangane da rawar da suka taka wajen bada rahotannin yadda zabukan 2019 suka rika gudana.

Ya ce wannan taron zai kara bada haske domin jin wasu abubuwan da suka gudana a lokacin zaben.

Shugaban NUJ na Kasa, ya ce a zaben 2019 ba a ci zarafin ‘yan jarida ba sosai kamar wasu zabuka na baya.

Ya ce taron na Abuja, na ‘yan jaridar da ke Arewa ne. Yayin da za a yi ba bangaren kudancin kasar nan a Lagos, nan na da dadewa ba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.