Labarai

Mun Gaji Da Zura Ido Ana Kashe ‘Yan Arewa A Yankin Kudu, Cewar Sanata Wamakko

Daga Tukur Sani Kwasara
Tsohon Gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta tsakiya Dr Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kakkausar suka ga kungiyar IPOB da kuma shugabannin kabilar Ibo na kudancin Nijeriya akan kisan ‘yan Arewa a kudu.

Wamakko ya ce” Ku daina fakewa da ‘yan kungiyar IPOB kuna kashe mana al’umma, ku sani cewa ba za mu lamunci hakan ba”.

“Hakurin da muke yi akan abubuwan da ake yi wa ‘yan Arewa a kudancin Najeria ya kare”.

“Mun baiwa matasan mu na Arewa hakuri lokuta da dama akan abubuwan da ke faruwa, kuma sun saurare mu da kunnuwan basira. Saboda haka doli ne mu tashi tsaye mu kare martabar su da kimar su”.

“Don haka idan baza ku iya yi wa matasan ku gargadi ba to mu ma zamu bar matasan mu na Arewa su yi abin da ya dace”.

“Saboda haka ku sani cewa lokacin yin shiru ya wuce, dole ne mu fito mu gaya muku gaskiya kokuna so ko baku so”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: