Labarai

Mun dawo da karfinmu – Wenger

Arsene Wenger na shan matsin lamba daga wasu magoya bayan Arsenal kan ya bar kungiyar
Kociyan Arsenal Arsene Wenger yana ganin yadda suka yi a wasansu na dab da na kusa da karshe na Kofin FA da Lincoln City ranar Asabar, sun farfado daga rashin katabus din da suke.
Kociyan yana ganin yadda suka bullowa wasan wanda suka ci 5-0 a Emirates, musamman ma bayan hutun rabin lokaci, sun farfado daga takaicin casa su da Bayern Munci ta yi, a gidan nasu 5-1, a gasar Kofin Zakarun Turai ranar Talata.
Kociyan dan Faransa ya ce, a kwanan nan ba su da wani katabus da kwarin guiwa, sakamakon rashin nasarar da suka yi ta gamuwa da ita.
Wenger mai shekara 67, wanda ke shan matsin lamba daga wasu magoya bayan kungiyar kan ya ajiye aiki, ya yaba wa kungiyar ta Lincoln, kan nasarar da ta yi ta zuwa har wannan mataki a gasar ta Kofin FA.
Lincoln, wadda ke matsayi 88, kasa da Arsenal a fagen wasa a Ingila 88, ita ce kungiya ta farko wadda ba ta cikin wata babbar gasa a Ingila da ta kai wasan dab da na kusa da krashe na gasar ta FA a cikin shekara 103.
An doke Arsenal a wasanta biyar daga cikin bakwai kafin wanda suka yi da kungiyar ta Lincoln City.
Wasu magoya bayan Arsenal na adawa da ci gaba da zaman Wenger a kungiyarHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionWasu magoya bayan Arsenal sun yi zanga-zangar adawa da Wenger kafin wasan nasu da Lincoln
Makomar Wenger wanda kwantiraginsa da kungiyar zai kare a karshen kakar da ake ciki, na cikin wani hali na rashin tabbas, sakamakon kosawa da wasu magoya bayan kungiyar suka yi da shi saboda rashin tabuka wani abin kirki da suke ganin Arsenal din na yi.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.