Hukumomi a Gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo sun ce an ceto gawarwaki kusan 500 bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa sun afka wa wasu ƙauyuka biyu a ƙasar ranar Alhamis
Bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, hukumomi suka ce an ceto gawarwaki kusan 500 a yankunan. Kusan kwanaki uku kenan tun bayan da ambaliyar ta afka wa wasu yankunan ƙasar, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane da dama. A baya dai hukumomin sun ce mutum fiye da 200 ne suka mutu.
A makon da ya gabata ma an samu matsalar ambaliya a wasu yankunan gaɓar tekun Kivu da ke makwabtaka da ƙasar Rwanda, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 100. A mafi yawan ƙauyukan da ke kusa da kogin Kivu, mutane kan yi tono cikin laka domin zaƙulo ‘yan uwansu da ke maƙale cikin lakar.
Ƙungiyar bayar da agaji da Red Cross a ƙasar ta ce ba ta da akwatunan da za ta saka gawarwaki, don haka ne take naɗe su a cikin barguna. Ruwa ya tafi da gidaje da dama. A ƙauyen Bushushu wasu daga cikin gine-ginen da har yanzu ke tsaye, kasa ta haɗiye kusan fiye da rabin tsayinsu.
Wata mata da ke cikin yanayin ɗimauta, ta ce duk da cewa mijinta ya samu kuɓuta daga ambaliyar, amma ruwan ya tafi da duka duka ‘ya’yanta.
It is heartbreaking to hear about the recent water contamination crisis in the Democratic Republic of Congo, where 400 people have fallen ill.
Add Comment