Mu Kyakyata

[MuKyakyata] A Yi Min Hadin Dambatta

Wani Bazazzagin saurayi ne ya taso takanas ta Kano ya zo har garin Kano don ya hada kayan lefen aurensa da za a yi nan da wata uku.
Saurayi ya shiga kasuwar Kantin Kwari, kasuwar da duk fadin nahiyar arewa ba ta da na biyu in dai wajen baje kolin atamfofi da yaduka ne.
Bazazzagin naku ya nufi wani katafaren shagon sayar da turamen mata yana cika yana batsewa wai shi ga shi mai da akwai tunda har kudi naira dubu hamsin ya zuba aljihunsa ya taho da su. Lefen naira dubu hamsin kuwa a garin Zaria ai sai ‘yar Saraki ko ‘yar tajiri.
Ko da shigarsa shago sai ya fara zaben atamfofi da leshi-leshi, dogwayen riguna da dai sauran kayan mata da ake zubawa a lefe. Gogan naku ya gama zabensa tsaf, sai ya kira mai shago don ya zo ya buga masa kudin ya zare ya biya
Mai shago ya dauki na’urar lissafi ya buga kudi tsaf, ya dago kai ya kalli Bazazzage wanda yana ta daga hanci, yana shakar iska wai shi ga isasshe. Mai shago ya ce “Yawwa Alhaji kudinka ya kama naira dubu dari hudu da arba’in da biyar da naira dari da hamsi, amma ka bar dari da hamsin din”
Bazazzage ya fitar da idanu ya ce meeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeee? A’a, a yi min hadin Dambatta

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.