Labarai

Mukadashin Shugaban Kasa ‘Osibanjo’ Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Nijeriya

Farfesa Yemi Osibanjo, Mukadashin shugaban kasar Nijeriya ya sanya hannu kan sabon dokar Fansho da Majalisa ta yi wa gyara da kuma wasu sabbin dokoki shida da ya tsallake karatun ta.
Sanata Ita Enang, Mataimakin shugaban kasa kan harkokin majalissu na musamman ya bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar, inda sanarwan ke nuna ayyukan da mukadashin shugaban kasa ‘Yemi Osibanjo ya aiwatar.
Dokoki shida da ya sanya wa hannu yana hade ne da tsaro, tantance fina-finai da kotuna, hukumar nazarin kimiya da kasa zata samar da kuma gyara a hukumar jingina