Wasanni

Muhammad Salah Ya Zura Kwallo Ta 100 A Firimiyar Ingila

Danwasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool kuma dan asalin kasar Masar, Mohamed Salah ya zura kwallo ta 100 a raga a gasar Premier League a karawa da kungiyar Leeds United ranar Lahadin da ta gabata.

Liverpool ta ziyarci Leeds United domin buga wasan mako na hudu a gasar Premier League, inda Salah ya fara cin kwallo a minti na 20 da fara wasan kuma kwallon da Salah ya ci ita ce ta 100 da ya zura a raga a Premier League, sannan ta biyar da ya yi bajintar a karancin wasanni, bayan Alan Shearer a wasa na 124, sai Harry Kane a karawa ta 141 da kuma Sergio Aguero a fafatawa ta 147.

Na hudu a wannan namijin kokarin shi ne Thierry Henry da ya ci kwallo ta 100 a Premier League a wasanni 160, sannan kuma sai Muhammad Salah wanda ya ci a karawa ta 162 kamar yadda kididdiga ta nuna.

Salah ya koma Chelsea da buga wasa a shekarar 2014, wadda ya fara buga wasa ranar 8 ga watan Fabrairu da ya shiga sauyin dan kwallo a fafatawa da kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United.

Wasa bakwai tsakani Salah ya fara ci wa Chelsea kwallo ranar 22 ga watan Maris a karawar da ta yi da Arsenal a Liberpool kwallo a Champions League a karawa da Hoffenheim a filin wasa na Anfield.

Kwana uku Tsakani, Salah ya ci kwallo ya kuma bayar an zura a raga a wasan da Liberpool ta doke Arsenal, sannan Mohamed Salah ya lashe kyautar takalmin zinare a matakin wanda ke kan gaba a cin kwallaye a Premier League a kakar wasa ta 2017 zuwa 2018 da kuma 2018 zuwa 2019.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement