Labarai

Mu Yi Koyi Da Halayen Manzon Allah (S.A.W, Kiran Gwamna Bala Mohammed Ga Musulman Nijeriya

… ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kasance masu tausayawa mata da yara kanana
A yayin da Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdukadir Mohammed ya halarci sallar Juma’a a masallacin Abu Huraira dake Wuse Zone 7, Abuja, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kasance masu adalci ga mata da yara da kuma mabukata.

Gwamnan wanda yake tare da rakiyar Maula Aliyu, a yayin zantawar sa da manema labarai bayan idar da sallar, ya kuma yi kira ga musulman Nijeriya da su kasance masu koyi da halayen Manzon Allah S.A.W wanda ya kasance mai jinkan mabukata a lokacin rayuwarsa.

Gwamna Bala ya kara da cewa addinin musulunci yana koyar da zaman lafiya, hadin kai da kuma neman ilmi ne, wanda hakan zai ba su damar gudanar da rayuwa mai kyau.

Ya kara da cewa ba wani yanki da zai samu ci gaba ba tare da ya daraja mata da matasa ba ta hanyar tallafa musu da kuma mara musu baya ba.

Kamar yadda Gwamna Bala ya ce, za a iya yakar talauci da jahilce ne ta hanyar sanya mata da matasa a harkar shugabanci a bangarori daban-daban.

Daga Lawal Muazu Bauchi
Mai taimakawa Gwamna Bala kan harkokin yada labaran zamani

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: