Labarai

Mu muka yiwa Buhari asiri – Inji wani dan Shi’a

A A Musa, ya bayyanawa shafin Hantsi24 cewa sune ke da alhakin yiwa shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari asiri Hoto: Facebook: Hatsi24.

Wani matashi dake bin mazhabar addinin Shia a jihar Kaduna wanda aka ambata da suna A A Musa, ya ce sune sukayi ma Buhari asiri.

Ya ce sunyi tattaki har jumhuriyar Nijar tare da tawagar malamai na kungiyar Shi’a.

Ya bayyana hakan a matsayin ramuwa kan abunda akayi ma shugabansu Ibrahim El-Zakzaky.

Wani matashi dake bin mazhabar addinin Shia a jihar Kaduna wanda aka ambata da suna A A Musa, ya bayyanawa shafin Hantsi24 cewa sune ke da alhakin yiwa shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari asiri saboda ramuwa akan abinda aka yiwa shugabansu Ibrahim Zakzaky.

 

A cewar Ahmad, sunyi tattaki har jumhuriyar Nijar tare da tawagar malamai na kungiyar Shi’a , inda suka dauki tsawon makonni uku suna iface-iface, kuma a ranar da suka dawo kasar ne aka kai shugaban kasar asibiti a karo na farko.

A cewar Hantsi24, lokacin da suka zanta da Ahmad ya bayyana masu cewa “Babu wata cutar kansa dake damun shugaban kasar!…mu muka rama abinda akai mana !..kuma wallahi Buhari bazai taba samun sauki ba, kuma idan mutun dan halak ne ya zage mu, wlh shima sai mun kaddamar masa !…inji Ahmad, wanda wata Majiya tace yana sana’ar sayar da magunguna a kemis.

 

SOuce In Hausa.Naij

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.