Labarai

Mu Muka Harbo Jirgin Yakin Nijeriya, Wanda Ya Bace Ba A Gan Shi Ba, Cewar ‘Yan Boko Haram

Daga Comr Abba Sani Pantami
‘Yan kungiyar Boko Haram, bangaren Abubakar Shekau, sun dauki alhakin baro jirgin yakin hukumar Sojojin Najeriya Alpha Jet NAF475.

Za ku tuna cewa a ranar Laraba hukumar sojin sama ta bayyana cewa jirginta ya bace a sararin samaniya a jihar Borno.

An tura jirgin taimakawa Sojojin kasa dake yakin yan Boko Haram.

Da safiyar Juma’a, hukumar Sojin saman Najeriya, NAF, ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna mata cewa jirgin yakinta Alpha Jet (NAF475) da ta bace a sararin samaniya ta yi hadari.

Kakakin hukumar NAF, Edward Gabkwet, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.

Da yammacin Juma’a kuwa, yan ta’addan Boko Haram suka saki bidiyo inda yake ikirarin su suka baro jirgin

A cewar HumAngle, bidiyon da Boko Haram ta saki ya nuna mambobin kungiyar rike da rokoki da kuma gawar daya daga cikin matukan jirgin da suka baro.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: