Mu Kyakyata

[Mu kyakyata] Shooting Film

M
U
S
H
A  Dariya.???

Naje wani restaurant ne cin Abinci,bayan an kawo min na fara kenan sai ga wani Alhaji ya shugo shima…yasha babbar riga da wata jaka a hannunsa ya nemi waje ya kame.

Can…sai ga wata mata ta shugo,taje ta durkusa a gabansa tana kuka tana cewa;

Don Allah Alhaji ka taimakeni…mahaifina ne baida lapia,gashi bamu da kudin da zamu kaishi asibiti…

Sai ya bude wannan jakar ya dauko naira miliyan daya ya bata…
Tayi masa godiya ta tafi.

Can….
Sai ga wani mutum shima yazo ya durkusa yace;

Alhaji…
Dan Allah ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimake ka…Alhaji,an koreni ne a gidan da nake haya…gashi bani da kudin dazan kama wani gidan…ga iyali…ga kudin makarantar yara.

Sai Alhajin ya bude jaka ya dauko miliyan biyu ya bashi,shima ya tashi ya tafi.

Ina kallon duk abinda yake faruwa…
Sai nima nace bari naje nayi wata Qaryar ko Allah zaisa na sami rabona!!!

Nan take na tashi naje na durkusa a gabansa na fara kuka….
Sai naji wani ya ta6ani yace;

Malam,Dan matsa… Muna SHOOTING FILM NE.

?????????

In Kaine…ko kece ya zakayi?

???

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.