Mu Kyakyata

[Mu Kyakyata] Saurayi Da Budurwa Ana Ruwa

MUSHA DARIYA
????⛄?
wani saurayine yaje zance wajen budurwarsa , suna tsakiyar hira sai aka fara ruwa kamar da bakin kwarya☔☔⛅ har zuwa dare ?ruwa bai daukeba.
 sai baban yarinyar nan yace da ita “naga alama ruwannan ba mai daukewa bane yanzu,don haka ki gara masa dakin bakin nan sai ya kwana anan idan  Allah ya kaimu gobe☀☀ sai ya koma.

budurwar ta mike ta shiga gida don cika umarnin mahaifinta. bayan ta gama gyara dakin sai ta dawo don yiwa saurayin nata iso  amma abin mamaki sai ta tarar bayanan don haka ta koma ta sanar da babanta halin da ake ciki.
 uban ya rinka mamakin inda ya shiga ana cikin haka sai gashi ya shigo da gudu jikinsa ya jike jagab, da ganinshi sai uban ya tmbaye shi ina yaje haka cikin ruwannan? sai saurayin nan ya amsa da cewa”ai gida na koma na dwakko bargo saboda ko za’ayi sanyi cikin dare ???wai idan kaine uban yarinyar ya zakayi?

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.