Mu Kyakyata

Mu Kyakyata: Rikitaccen Tsoho

RIKITACCEN TSOHO. ??????
wani saurayi yana tafiya a hanyarsa ta zuwa
rumfar mai abici, sai ya hangi wani tsoho sai
sharbar kukansa yake ba kakkautawa, sai
tausayin wannan tsoho yakamashi.
Sai ya nufi wurin tsohon:
baba lafiya kake irin wannan kuka haka? Sai
wannan tsoho yece:yaro ina da mata yar
kimanin shekara(22)a gida.
kullum da safe sai ta
yimin tausa’ kuma ta soya min kosai ta yimin
koko ta kuma dafamin shayi mai dadi.sai
saurayin yace to me yasa kake kuka?.
Tsohon yace:Da rana kuma tayimin miyar
alayyahu da tuwon shikafa mai dadi ta kuma
hadamini zobo mai sanyi,ta kuma tsaftace
gidan.bayan ta gama, sai tazauna kusa dani
ta kunna mana talabijan
muyi kallo cikin jin dadi har yamma. sai
saurayi
yace baba har yanzu baka fadamin abinda
yasa kake kuka ba!.
sai tsoho yace: da daddare kuma tayimin
alkubus da romon kaza’ta kuma matse lemo
ta kawo min, naci na sha
cikin annashuwa. sai wannan saurayi yace
to duk da wannan abu da take maka me
kuma
yasaka kuka baba?.sai tsoho yace: to ai
hanyar
gidan na manta???????

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.