Mu Kyakyata

[Mu Kyakyata] MALAMIN ISLAMIYYA A SECONDRY

 MUDAN DARA AYI RAHA
.
Wani malamin islamic ne awata sakandire, ya kwashe tsawon lokaci yana koyama daliban ss 2 darasin tarihin, sai wata rana ya yanke shawarar bara ya gwada daliban nan ya gani, suna gane tarihin musulimci sosai kuwa.
.
Sai ya tambayi wata daliba dake zaune a gaba gaba, mai suna jummai, yace ”jummai wa ya kashe ABU JAHAL?” cikin razani ya rinya ta mike tace ”wallahi malam bani bace don yau ma amakare nazo” cikin bacin rai malamin ya kauda kansa.
.
ya tada wani dalibi dake can baya, mai suna mubarak yace’ ”mubarak gayamin waya kashe Abu jahal?” yaron yatashi jikinsa na rawa yace
”Wallahi malam bansan wanda ya kasheshi ba, don mima tunda nashigo ajin nan nake gyangyadi,” Ran malamin ya kara baci.
.
ya juya zai fita ajin kenan, sai ga wata daliba ta shigo wadda duk ajin bamai kokarinta, malamin yayi murmushi aransa yace gamai bada amsa nan, yace SUWAIBA waya kashe abu jahal?” yarinyar ta zazzaro ido ta dafe kirji, tace Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, yaushe aka kasheshi? Allah yaso zuwa na kenan, malamin ya fice ajin a fusace, ya nufi ofishin principal din makarantar.
.
ya kwashe labari ya gayamai yanda sukai da dalibansa, cikin fushi shima principal din yace muje ajin, suka dawo, principal yace maimaida tambyar, malam yace waya kashe Abu jahal? Aji sukayi shuru cirko cirko, ya sake tambaya waya kashe abu jahal?, aji shuru sai zare ido suke, ya sake tambaya akaro na uku, waya kashe abu jahal? Shuru dai, can sai principal din ya kalli malamin yace ”ANYA KUWA KANA GANIN ACIKIN AJIN NAN AKAYI KISAN NAN”?
.
Wai inkaine mezaka cema wan nan principal??

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement