Wani mutun ne me suna Hambali yana neman sana’a sai ya samu aiki a filin koyon jirgi, aikin sa shi ne share-sharen ciki da wajen jirgi. kwatsam, ranar nan yana cikin shara sai ya tsinci wani dan littafi. A rubuce a jikin littafin an rubuta koyon jirgi a saukake.
Yayi murna kwarai, sai ya wuce gun da dereba ke zama ya ga wasu madannai birjid a guri daya sai ya buda littafin shafin farko sai ya ga ansa idan kana son kunna jirgi danna fari sai ya danna jirgin ta tashi.
Ya bude shafi na biyu sai ya ga an ce idan kana son kofofin jirgi su rufe danna kore sai ya danna kofofin suka rufe haka yayi tayi har dai lokacin da ya tsinci kan shi a sararin samaniya yana ta keta hazo, a lokacin da ya bude shafin karshe sai ya ga an rubuta saukar jirgi sai a littafi na biyu.
Toh idan kai/ke ne ya za ka/ki yi?
Add Comment