Mu Kyakyata

[Mu Kyakyata] Mai Gida Da Matarsa


*MUSHA DARIYA HAHAHA..*
Wani magidanci ne yana hira da matarsa sai yacemata:
Honey gaskiya budurwata Aisha tana qaunata sosai.
Matar tace masa, Gaskiya Aisha budurwarka ta burgeni. 
Maigidan nata yace, Rannan fa har cemin tayi honey na yadace muje Wellcare domin muyi siyayyar kayayyaki.
Sai matar tace gaskiya ta burgeni. 
Sai mai Gidan nata yace, Jiya fa har cemin tayi honey I love u very very much ❤❤❤❤❤.
Sai matar tace masa, Gaskiya budurwarka tana sonka. 
Sai mai Gidan yace dazu kuwa tacemun, Ina my son (danki)? Kinsan tafiki Qaunarsa.
Sai matar tace gaskiya ta burgeni. 
Qarshe dai sai mai gidan yacemata, Wai ke Sadiya babu abinda yake bata miki rai ne?
Budar bakin matar sai tace, Eh babu abinda zance. Ai na ganeka. *Duk BUHARIYYA ce. So kakeyi muyi fada ka korani gida. Ba inda zani.*

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.