Mu Kyakyata

[Mu Kyakyata] Mai Abinci Da UstaZ

Akwai wata mai abinci data kware wajen iya girki, matsalarta kawai masifa da ruwan bala’i. Rannan sai wani Ustaz yazo cin abinci, da ya kammala cin abinci sai mai karbar kudi tace malam kudin ka dubu daya da dari daya…
anan fa Ustaz ya kafe yace bazai biya ba domin kudin yayi yawa….
Yarinya da taga abu yafi karfinta saitaje gayawa Hajiya…..
 tun daga wajen shago Hajiya ke danna zagi da masifa tace bari inga wane shege ne zai kawomin iskanci da raini..
 tana shiga shagon sai ta hada ido da Ustaz sai kawai tayi shuru ai sai takoma kan mai karbar kudi da masifa kefa baki da lissafi ai sai kiyi min bayani kice Mallam ne ai…
 Sai tace kara mar Special Pack biyu ki hada masa da ruwan Swan guda biyu…….
 mai aiki tayi shiru tana mamakin Hajiya………
 sai da Hajiya ta daka mata tsawa sannan ta dawo hankalinta… ta hada abinci tabawa Ustaz….
 Hajiya sai ta fara cewa an gode Mallam Allah yasaka da alheri……
 Ustaz na fita Hajiya ta fadi kasa tana hada uban gumi tana wani irin nishi…..
 sai mai aiki tace Hajiya lafiya kuwa…..
 Hajiya tace baki gane shi ba? SHEKAU ne ai DAN Ubanki…?????

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.