Mu Kyakyata

[Mu Kyakyata] Dubun Na Bashi

DUBUN NA BASHI…
Wani limami ne ya tashi babu kudin cefane har yamma tayi #20 kawai ke gareshi duk abin duniya ya dameshi, har aka kira sallar la’asar, kawai sai wani bawan Allah ya kira liman ya bashi gudan #1000 sadaka, ai nan take hankalinsa ya dawo har ya tuna an kira sallah, nan take ya tare dan achaba xuwa masallaci, koda isar su yana sauri ya saka hannu a aljihu ya dauko wannan gudan #1000 a tunaninsa #20 ne, ya mikawa dan achaba, sai mai mashin abin ya bashi mamaki har ya tambayi mallam cewa tsaya in baka chanji, sai mall yace babu komai rike na baka, liman na tunanin ko #20 ne ya bashi, liman na sauri domin ya makara, yana shiga bayan an tayar da sallah, hmmmmmm koda liman yayi sujjada sai #20 dake gaban aljihunsa ta fado, koda liman ya gani sai yayi salati da karfi yace ( KAN UBAN CAN) jama’a dubun na bashi!

Rubutawa :
Haiman Khan Raees
@HaimanRaees

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.