Wata Mahaukaciyace tana zaune a
gefen titi tana ta muzurai da
sumbatu. Sai ta hangi wata
Bafulatana dauke da kwaryar nononta
ta fito talla, sai mahaukaciyar
tace,”Ke mai nono, kawo”. Bafulatana taje ta sauke kwaryar
nonon a gaban wannan matar, sai
bayan ta ajiye sai taga ashe
mahaukaciyace, ga kuma wata
katuwar sanda akusa da ita sai zare
idanu take babu alamun sauki a tare da ita. Cikin tsawa mahaukaciyar tace da
Bafulatana “nawa-nawa?” Jiki na rawa bafulatana tace “kona
nawa kikeso ai sai a baki “. Mahaukaciya tace “To auno na naira.” cikin rawar jiki Bafulatana ta auno
dayawa sai tace mata gashi. Sai ta
sake daka mata tsawa tace “Kyauto!” Bafulatana ta sake kamfatowa ta
zuba, sai gogar tace mata “To
shanye!” Bafulatana ta dauka ta
shanye. Mahaukaciya ta kara cewa kara
aunowa, ta kuma cewa ta kyauta, ta
kara zubawa sannan ta kuma cewa ta
shanye. Bafulatana ta kuma dauka ta kuma
shanyewa Mahaukaciya ta kara cewa
ta auno a karo na uku. Sai shima ta
shanye daga nan kuma sai ta daka
mata tsawa tace “Yan banza, ashe
kuna so kuke kaiwa kasuwa? ” Tashi ki bani guri. Bafulatana ta suri kwarya
ta hanzarta barin gurin. To wannan shine asalin karin maganar
da ake cewa “ANASO ANA KAIWA
KASUWA.
Rubutawa :
Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
Add Comment