——ANJI KUNYA——- Wani saurayi ne yaje gaishe da sirikansa. Bayan ankaishi falo sun gaisa da sirikan nasa, da yan’uwan budurwar, sai aka kawo masa cin~cin da drinks. Amma yaki sha akayi juyin duniya dashi dan yaci cin~cin din nan amma yaki ci. Sai iyayen yarinyar da yan uwanta suka fita tsakar gida suka barshi suka ce “kila kunyarsu yakeji shiyasa yaki ci” itama yarinyar tace bari inbaka guri kaci. Sai itama ta fita, sai ya dauki kwanon cin~cin din ya juye rabi a cikin hularshi, ya maida ita. Bayan ta dawo yace mata zai tafi tace kadai kin cin komai yace mata na koshi ne. me zai faru, ya fito tsakar gida suna bankwana da iyayenta, kawai sai yaci karo da igiyar shanya, aikuwa hula ta fado sai ga cin~cin Shaaaaaaa!. yana zubowa sai gayenka ya karkace yace “ikon Allah yau kuma ruwan cin~cin akeyi”…………. ???????
[Mu Kyakyata] ANJI KUNYA-
January 4, 2017
134 Views
1 Min Read
You may also like
Musha Dariya: Su Bafulantani An Shigo Birni
January 28, 2018
Mu Kyakyata: Rikitaccen Tsoho
July 30, 2017
[Mu Kyakyata] Wani Bazazzage Da Alawar Sweet Campo
March 21, 2017
Mr. ArewaBlog
C.E.O/Founder ArewaBlog
Add Comment