Daga Abdurrahman Abubakar Sada
Hanya mafi kyau, kuma mafi sauki da za mu takaitar da yaďuwar alfashar luwaďi a cikin al’ummah, ita ce; zaben shugabanni masu tsarki.
Duk wanda ya zabi ďan luwaďi, to duk luwaďin da aka yi cikin mulkinsa, sai an rubuta maka kamisho (da hannunka a ciki).
Ba luwaďi kaďai ba, duk wani nau’in sabo da Allah ya hana, to ka guji zaben shugaban da zai jaddada wannan sabon.
A Al-Kur’ani Allah ya faďa mana cewa: “Idan ya yi nufin halakar da alkarya, to sai ya sanya manya (shugabanni da masu faďa aji), su tsunduma cikin fasikanci da sabon Allah, sannan sai halaka ta biyo baya”.
Hakki ne a kan kowa, ya zabi shugaba na gari, sannan ya bi shi da addu’a da fatan alheri, to a nan ka sauke nauyin da Allah ya ďora maka.
Mu masu kira ne da faďakarwa, ya rage wa mai kallo da karantawa, ko dai ya gasgata a nan, ko a can.
Allah ya zaba mana na gari.