Rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewa tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho, ya tattauna da tsohuwar kungiyarsa ta Inter Millan akan komawa kungiyar.
Mourinho, wanda ya lashe kofin firimiya da gasar cin kofin zakarun turai a Inter Millan kafin ya koma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid yanason komawa babbar kungiya ne tun bayan barinsa United din.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Mourinho ya tattauna da shugabannin kungiyar a kokarin da yakeyi na maye gurbin Luciano Spaletti, wanda a yanzu shine kociyan kungiyar kuma kungiyar bata gamsu da salon aikinsa ba.
Inter Millan wadda a yanzu take mataki na uku akan teburin na Siriya A bata samu damar cigaba da buga wasan zakarun turai ba a zagaye na biyu kuma kawo yanzu babu tabbas din zata sake komawa gasar a kakar wasa mai zuwa.
- Advertisement -
Kawo yanzu dai Mourinho baya aiki da kowacce kungiya duk da cewa kungiyoyi da dama irinsu tsohuwar kungiyarsa Benfica ta yi masa ta yin aikin koyar da kungiyar inda yaki amincewa da karbar aikin.
A kwanakin baya dai Mourinho ya bayyana cewa bashi da niyyar karbar karamar kungiya inda ya bayyana cewa har yanzu yana da karfin da zai cigaba da koyar da manyan kungiyoyi a nahiyar turai kuma ya ce bazai karbi aikin koyar da kasa ba.
#Hausaleadership