Akwai nau’ukan motsa jiki da dama, amma akwai na musamman da suka shafi ƙarin lafiya ga rayuwar jima’i ga ɗan Adam.
Motsa jiki wani ɓangare ne na musamman na kiwon lafiya wanda yin sa ke tasiri ga ƙara ƙoshin lafiya, rashinsa kuma ke zama illa ga lafiyar.
Motsa jiki kan kasance maganin cututtuka da dama, waɗanda likitoci ke bai wa mutane shawara su dinga motsa jikinsu saboda muhimmancinsa ga lafiya.
Ƙwararren likitan motsa jiki (Physiotherapist) Dakta Abubakar Ahmad Tsafe na babban asibitin Farida da ke Gusau a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, ya yi bayani kan wani nau’in motsa jiki da ya shafi lafiyar jima’i da inganta al’aurar maza da mata.
Likitan ya ce irin motsa jikin zai taimaka wa maza magance matsalar saurin inzali ko gamsuwa da wuri lokacin jima’i da rashin ƙarfin al’aura da masu matsalar da ta shafi mafitsara, haka kuma ga mata motsa jikin na inganta ƙarfin jijiyoyin ƙugunta zuwa ga gabanta.
Kegel
Likita Abubakar Ahmad tsafe, ya ce mafi kyawun magani shi ne motsa jiki.
Motsa jikin da ake kira Kegel wani nau’in motsa jiki ne mai sauƙin yi wanda ake yin sa domin ƙarfafa jijiyoyin ƙashin ƙugu da ake kira pelvic ga mata da maza.
Pelvic kuma wuri ne tsakanin ƙugu ko kwatangwalo da ke riƙe da al’aurar mace ko namiji.

A wani cikakken bayani da ta yi game da motsa jikin kegel ga maza da mata, uMujallar Lafiya ta Healthline ta ce motsa jikin na taikamaka wa gaɓoɓin ƙashin ƙugu (pelvic) haɗi da inganta kulawar mafitsara da kuma ƙarfin jima’i.
Sannan ana yin motsa jikin Kegel ne domin ƙara wa jijiyoyin ƙashin ƙugu ƙarfi, domin rauninsu na iya haddasa rashin iya sarrafa mafitsara da matsaloli na rashin ƙarfin jima’i da rashin samun gamsuwa
Dakta Tsafe ya ce idan ana irin motsa jikin kegel yana ƙara wa jijiyoyin da ke riƙe da pelvic karfi, idan suna da rauni.

Amfanin Kegel ga maza
Dalilai da dama kan haddasa rauni ko rashin ƙarfin ƙashin ƙugu, domin a lokacin da mutum yake saurayinsa suna da ƙarfi yayin da kuma yake ƙara manyanta za su samu rauni wanda kuma zai yi tasiri ga rayuwarsa ta jima’i.
Mujallar lafiya ta Healthline ta ce, bincike da dama da aka gudanar ya nuna cewa ga maza, motsa jikin kegel na magance matsalar rashin ƙarfin gaban namiji da kuma hana saurin inzali. Haka kuma yana ƙara wa maza daɗin jima’i da sha’awa.
Dakta Tsafe ya ce motsa jikin kegel na da amfani ga zagayawar jini, kuma yana ƙara gina jijiyoyi da ƙashin ƙugun namaji, su kasance masu ƙarfi sosai.
“Idan kana motsa jiki za ka daɗe ba ka kawo ba a lokacin saduwa da iyali,” in ji likitan.
Ya kuma ce ga waɗanda ba su iya riƙe fitsari, idan suna motsa jikin zai taimaka masu sosai
Amfanin Kegel ga mata
Ga mace, matsaloli da dama kan haifar da rauni ga jijiyoyi da ƙarfin naman ƙashin kugu musamman sakamakon ciki ko haihuwa ko kuma matsalar mafitsara ko tiyata a mafitsara.
Amma ta hanyar motsa jikin Kegel yau da kullum, likita ya ce mace za ta iya ƙarfafa jijiyoyin ƙashin ƙugu, wanda kuma zai yi tasiri sosai.
Dakta Tsafe ya ce motsa jikin kegel na ƙara inganta zagayawar jini zuwa pelvic da kuma gaban mace – saboda motsa jikin zai taimaka ya fitar da duk wani datti da ke wurin, ba tare da wani abu ya rage a mafitsara ba.
“Zai kasance jijiyoyin da ke wurin suna da ƙarfi – kuma lokacin da suka je fitsari gaba daya zai fita ba zai takura wa pelvic da kuma wata damuwa ba.”
“Motsa jikin kegel na ƙara wa mata ni’ima, kuma yana taimaka masu su ƙara samun gamsuwa da jin daɗin jima’i,” in ji likitan.


Kafin fara motsa jikin kegel
Lokacin da za a fara yin motsa jikin, an fi son a fara gano asalin jijiyoyin da suka dace da gefen da suke ta hanyar wasu dubaru.
Mujallar Healthline ta ce za a iya ganowa ta hanyar sanya yatsa mai tsabta a cikin farji tare da matse jijiyoyin farjin a tsakanin yatsan.
Wata hanyar kuma ga maza da mata ita ce ta hanyar ƙoƙarin katsewa ko riƙe fitsari a yayin da mutum ke tsakiyar yin fitsarin, ko kuma rike ba-haya.
Jijiyoyin da mutum ya yi amfani da su wajen riƙe fitsarin su ne na ƙashin ƙugu da mutum zai iya fahimta a gefen da suke – su ake son a motsa don ƙara inganci da ƙarfi ta hanyar motsa jikin kegel.



Ire-iren motsa jikin kegel
Akwai hanyoyi daban- daban na motsa jikin kegel – za a iya yi daga tsaye ko daga zaune ko a kwance.
Mafi yawanci wanda aka fi yi shi ne wanda mutum zai kwanta yana kallon sama, sai ya ɗago ƙugu sama, hannu a miƙe a ƙasa an lanƙwashe guiwa.
Dakta Tsafe ya ce za a iya yi kamar daƙiƙa uku zuwa biyar sai a numfasa kuma a sake ɗaga ƙugu sama.
Irin wannan mata da maza duka za su iya yi.
Na zaune


Akwai kuma wanda za a zauna kamar zaman cin tuwo a lanƙwashe ƙafafu ɗaya na saman ɗaya.
Wannan ma za a iya yi na ɗan wani lokaci ana hutawa ana sake yi.
Na duƙe


Akwai wanda za a yi daga duƙe inda za a yi goho a ɗaga ƙafa sama musamman gefen jijiyar ƙashin ƙugu, gwiwar ɗaya kafar kuma a ƙasa
Rub da ciki


Akwai wanda za a yi kamar rub da ciki amma a mayar da hannu baya a riƙe kafafu da hannayen.
Likita ya ce da zarar an fahimci yadda ake Kegel za a iya yinsa a kowane lokaci kuma a ko ina – cikin gida ko wani wuri keɓaɓɓe a wurin aiki.
Mutum na iya yi sau biyu a rana da safe da yamma, ko kuma lokacin duk mutum yake da dama.
Kuma akwai ire-iren motsa jikin Kegel da dama fda mutum zai iya yi idan har ya fahimci gefen da jijiyoyin pelvic suke.
Add Comment