Kocin Manchester United, Jose Mourinho, ya ce ta yiwu ya zama dole shi ya kara sayan dan wasa daya kawai domin kasuwar ‘yan wasa na da wuya.
Dan asalin kasar Portugal din ya nuna cewar kulob-kulob na tsawwala farashin ‘yan wasa a kasuwar lokacin bazarar.
Mourinho ya ce: “Ba mu shirya wa biyan abin da kulob-kulob din suke so ba.”
Kocin Chelsea din, wanda ya sayi ‘yan wasa biyu bayan ya nemi hudu daga kungiyarsa, ya ce: ” Na saba ganin kulob-kulob na biyan makudan kudade wajen sayen ‘yan wasa.
A halin yanzu kowa na biyan makudan kukade kan ‘yan wasa masu kyau.”
United ta kashe Fam miliyan 75 kan dan wasan Everton, Romelu Lukaku, tare da kashe Fam miliyan 31 kan dan wasan bayan Benfica, Victor Lindelof, tun karshen kakar bara.
Sayen dan asalin Belgium, Lukaku, ya sa jumullar kudin da kulob-kulob din gasar Firimiya suka kashe a kasuwar ‘yan wasa ta wannan lokacin ya zarta Fam miliyan 500.
Kamfanin lissafin kudi na Deloitte ya ce kungiyoyin gasar Firimiya suna kan hanyar wuce tarihin da suka kafa na kashe Fam dala biliyan 1.165 da suka kashe a lokacin bazarar da ya wuce.
Add Comment