Modric Zai Bar Real Madrid A Kakar Wasa Ta Gaba
Kungiyar kwallon kafa ta Inter Millan ce dai take neman dan wasa Modric ruwa a jallo inda ta zuba masa makudan kudade idan har ya amince zai koma kungiyar sai dai Real Madrid tayi nasarar hanashi tafiya. Sai dai ana ganin dan wasan tuni ya mayar da hankalinsa wajen ganin yabar kungiyar kuma ana zaton a kakar wasa mai zuwa dan wasan zai bukaci Real Madrid data bashi damar zuwa Inter Millan din.
Tuni dai daman Real Madrid ta fara canja yanayin yadda take siyan ‘yan wasa zata koma siyan matasan ‘yan wasa tana cike gurbin manyan ‘yan wasan da suka bar kungiyar kuma ta fara akan dan wasa Cristiano Ronaldo bayan kungiyar ta siyo Mariano Diaz domin ya maye gurbinsa.
A shekara ta 2020 dai kwantaragin dan wasan zai kare kuma tuni kungiyar ta yanke shawarar cewa bazata karawa dan wasan shekara sama da daya ba saboda ya kai shekara 30 kuma yanzu yana fama da yawan zuwa ciwo.
Duk da cewa magoya bayan kungiyar suna son dan wasan wanda shine gwarzon dan wasan Fifa na wannan shekarar kuma ana zaton shine zai lashe kyautar gwarzon Baloon ‘d’O ma da kamfanin jaridar zaibaya a watan Disamba.
Inter Millan dai sun yiwa dan wasan alkawarin shekara hudu idan yakoma kungiyar kuma zata bashi albashin fam miliyan tara idan har ya amince da komawa kungiyar ta kasar Italiya kuma tayi masa alkawarin zata bashi dama yayi ritaya a kungiyar.
#Leadershipayau