Ministar Kudi Zainab Shamsuna Ahmad ta karbi bakuncin jami’an hukumar USAID da na shirin bunkasa samar da wutar lantarki na kasa, bisa jagorancin Stephen Haykin.
Manufar shirin shine bunkasa samar da wutar lantarki tare da warware matsalolin dake hana ruwa gudu wajen samun masu zuba jari a bangaren.
A jawabinta, Ministar ta bayyana cewa gwamnati zata cigaba da marawa shirin baya ta hanyar samar da yanayi daidaitacce don samun karin zuba jari a bangaren iskar gas, samar wa da raba ingantacciyar wutar lantarki tare da samar da wutar a wuraren da babu.