Minstar Kudi Zainab Shamsuna Ahmad na halartar taron da ake gudanarwa na Bakwai da masu ruwa da tsaki akan aiwatar da nagartattun manufofin tarawa da kashe kudade yadda ya kamata, tare da kwamishinonin tsara kasafin kudi na Jihohi, mai taken “Cimma Zahiri ta fuskar shirya kasafin kudi a matakin Jihohi da na Tarayya don aiwatar da ingantattun aiyuka”.
Tasirin wannan taro shine kara bunkasa basirar kwamishinonin tsara kasafin kudi na Jihohi don gudanar da aiyukansu yadda ya kamata tare da musayar bayyanar da kara dankon zumunci da aiki tare.
Daga cikin abubuwan da aka tattauna a wajen taron akwai batun kara fadada zauren don saka Ministar Kudi da kwamishinonin Kudi na Jihohi a cikin zauren don inganta tsarin shirya kasafin kudi da tafiyar da harkokin kudin yadda ya kamata.