Kimiyya

Ministan Sadarwa Sheikh Pantami, Ya Bada Umurnin A Cigaba Da Rajistar Sabbin Layuka

…Dole sai mutum ya nada lamban katin zama dan kasa, kafun a mishi ragista.

Daga Comr Abba Sani Pantami

Gwamnatin tarayya ta bada izinin cigaba da rajistan sabbin layukan waya bayan wata da watanni da sanya takunkunmin yin haka.

Ministan Sadarwa da tattalin Arziki na Digital Sheikh Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa, Dr Femi Adeluyi, ranar Alhamis a shafin Tuwita.

Ministan ya ce za’a cigaba da rajistan amma da sharadin sai mutum na da lamban katin zama dan kasa, NIN.

Pantami ya ce an yanke shawaran cigaba da rijistan sabbin layuka ne bayan amincewar shugaba Buhari da sabon tsarin rijistan layuka da ma’aikatarsa ta samar.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement