Minista Ya Ajiye Mukaminsa Bayan Wani Dan Jarida Ya Bankado Wata Badakala Da Ya Shirya


1 193

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Karamin Minista Mista Rockson Bukari ya ajiye aikinsa nan take, bayan da wani dan jarida ya yi dauki murya (Recording) din wayar da suka yi, wacce a ciki ya ke kokarin ba wa dan jaridar cin hanci a kan kada ya wallafa wani labarin da zai bankado cin hancin dake faruwa a hukumar kula da albarkatun kasa dake kasar.

Kamfanin hako ma’adinai na Shaanxi Mining Company na mutanen China, su ne suka hada kai da Ministan wajen aikata cuwa-cuwa, shi kuma dan jaridar ya samu cikekken rahoto akai, shi kuma minista sai ya yi kokarin bawa dan jaridar cin hancin da zai siye bakinsa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Tuni dai Minista Bukari ya ajiye mukaminsa, har shugaban kasar, Nana Akufo-Addo ya amince da hakan.

Madogara: Rabi’u Rabiu Biyora

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.