Labarai

Minista Sheik Pantami Ya Amsa Tambaya Kan Ko Yana Goyon Bayan Ta’addanci

Daga Datti Assalafiy
Rigiji gabji babban goro sai magogin karfe, Tafsirin da Sheikh Dr Isa Ali Pantami ya gabatar yau Asabar na musamman ne, domin ya amsa tambayar da aka masa akan wasu jaridu da suka masa sharrin cewa wai yana goyon bayan kungiyoyin ta’addanci

Malam ya bada amsa da cewa; Duk wanda yake bibiyar karantarwansa kamar shekara 15 da suka wuce zuwa yanzu baya bukatar a bashi amsa akan ko yana goyon bayan ta’addanci, gaba daya da’awarsa ta tafi akan yaki da zalunci da ta’addanci ne

Malam yace ya rubuta takardu sama da guda 30 a jami’ar ATBU ya rabawa dalibai domin su nisanci shiga cikin kungiyar ta’addanci, Malam yaje har Masallacin Indimi a birnin Maiduguri yayi khuduba da muhadara akan nisantar ta’addanci, Malam ya tsallaka har Kasar Nijer garin Diffa yayi wa’azi akan nisantar ta’addanci na tsawon kwana uku, sannan yaje Katsina da wasu jihojin Arewa a lokacin da aka fara rikicin Boko Haram

Malam yace bai san adadin matasan da zafin kai ya shigar da su da’awar Boko Haram ba ya musu nasiha suka ajiye da’awar suka dawo kan gaskiya , yace idan an bashi dama ya kirga yawansu adadinsu ba zai kirgu ba

Malam yace jifansa da akeyi yanzu da kazafin cewa wai yana daukar nauyin ta’addanci ba wani abu bane illa manufa ta siyasa, yace a rayuwa duk lokacin da Allah Ya jarrabeka kake samun wata daukaka ko karbuwa a gurin jama’a to ba zai yiwu ka zauna lafiya ba, ko Masallaci ne kake Limanci Masallacinka yana cika to ba zaka zauna lafiya ba, zaka hadu da makircin mahassada

Malam yace irin wannan sharri da kazafi da ake masa baya tayar masa da hankali, damuwaraa shine neman yaddar Allah (SWT), Malam yace babban fatansa a yanzu shine kada Allah Ya bashi ikon cin amanar da shugaba Muhammadu Buhari ya bashi

Malam yace abinda nake fadawa masoyana da masu saurarona don Allah irin wadannan maganganu da ake min ban yadda ku zagi wani ba, ban yadda ayi wa wani kazafi ko a aibatashi ba, idan sun wallafa sharri a kaina a fada musu cewa kuskure ne su gyara, idan basu gyara ba mun barsu da Allah domin akwai wata rayuwar bayan wannan

Malam yace shi karantar da addini ya sa a gaba, wadancan tsoffin muhadara ko khuduba da ya gabatar a baya kan zaluncin da aka yiwa kasashen Larabawa fahimtace ta addini, Malam yace kuma tsarin mulki na kasa a matsayinsa na ‘dan Nigeria ya bashi ikon yin addininsa da kare martaban ‘yan uwansa Musulmi

Malam yace idan yayi fatawa ta addini ba ra’ayinsa bane, fahimtace ta addini, idan fahimtarsa ce yana iya dacewa yana iya yin kuskure, Malam yace idan kunga ya dace ku dauka, idan kunga bai dace ba ku bari, Malam yace shi kansa idan yayi fatawa daga baya ya gane akwai kuskure yana canzawa, yace a rayuwarsa ya canza fatawa tafi dari saboda ilmi kullun karuwa yake

Malam yace a matsayinsa na Musulmi baya goyon bayan ta’addanci, Malam yace idan wani ya kawo maganar cewa wai yana goyon bayan Taliban ko Al-qa’idah fahimtarsa ce wancan, amma shi kam a yanzu da yake magana ba fahimtarsa bane wannan

Malam yace akwai wadanda suke yawo da audio na maganganunsa lokacin da yake wayar da kan matasan Musulmi su guji shiga kungiyoyin ta’addanci, wasu muhadarorin yayi su tun shekarun 1990s, Malam yace shi ya fara karantarwa tun bai wuce shekaru 12 ba da haihuwa a duniya, wato tun kafin ya balaga, Malam yace mutumin da yake wa’azi tun kafin ya balaga mai zai hana yayi kuskure?

Malam ya tabo abinda ya shafi tsarin siyasa ta duniya da rikicin da akayi tayi, yace ai ko ‘yan siyasa sun canza matsayi, yakin da akayi da Afghanistan, Malam yace hatta shugaban Kasar Amurka na yanzu Joe Biden lokacin yana Sanata bai goyi bayan yakin Amurka da Afghanistan ba, Malam yace shima bai goyi bayan yakin ba, kuma kowaye za’a kashe a cutar dashi haka siddan bai goyon baya

Malam yayi gwalagwalan bayanai wanda suka cancanci a rubuta su da ruwan danyen zinare saboda fa’idarsu, Insha Allahu zamu tura audio a group na Whatsapp da Telegram kamar yadda muka saba.

Allah Ka tsare mana rayuwar Malam Isa Ali Pantami, Allah Ka kara masa girma da daukaka Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: