Wasanni

Messi Ya Yi Jawabin Bankwana Da Barcelona

Daga Sulaiman Ibrahim,
Lionel Messi ya yi bankwana da Barcelona bayan shekaru 21: “Ba na son barin wannan kungiyar, ina son kungiya ta”;

PSG ta yiwa Messi tayin kwantiragin shekaru biyu wanda zai kai £ 25m a shekara bayan haraji tare da zabin karin shekara.

Messi ya yi hawaye yayin da ya samu gagarumar tarba a taron manema labarai na karshe na Barcelona don sanar da karshen shekaru 21 da ya yi a kungiyar ta Barcelona.

Messi ya yi tattaki zuwa Barcelona yana tsammanin cewa za a amince da sanarwar sabuwar kwantiraginsa na shekaru biyar a Barcelona, bayan ya tabbatar da rage albashinsa da kashi 50 cikin 100.

Nasarorin Da Messi Ya Samu A Barcelona

Messi ya ce “A bana, ni da iyalina mun gamsu cewa za mu zauna a Barcelona, abin da duk muka fi so kenan”.
“Muna tsammanin za mu zauna a nan Barcelona. Amma a yau, dole ne mu yi ban kwana da duk wannan tunanin.”

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement