Wasanni

Messi ya bai wa PSG haƙuri kan tafiyarsa Saudiyya

Messi ya bai wa PSG haƙuri kan tafiyarsa Saudiyya
GETTY IMAGES

Messi ya bai wa PSG haƙuri kan Tafiyar Shi Saudiyya

Lionel Messi ya nemi ahuwar abokan kwallonsa na PSG tare da yanzu yana jira ya ga hukuncin da ƙungiyar za ta yanke kansa bayan tafiyarshi Saudiyya.

An dakatar da kyaftin ɗin Argentinan na mako biyu saboda tafiyar da ya yi ba izini.

Wannan na zuwa ne bayan rashin nasarar da PSG din ta yi a gida a hannun Lorient a ranar Lahadi – rashin nasara na uku kenan cikin wasa shida kusa-kusa – kuma Messi ya buga minti 90 na wasannin dukka.

“Ina ba da haƙuri kan abin da na yi, ina jiran hukuncin da kulob zai yanke a kaina,” Yadda Messi ya bayyana a wani bidiyo da ya wallafa a Instagram.

“Gaskiya na yi tsammanin za mu samu rana guda ta hutu kamar yadda muka saba a makonnin baya.

“Na shirya tafiyar nan zuwa Saudiyya a baya ina sokewa. A wannan karon ba zan iya sokewa ba.”

Messi ya shirya barin PSG din a ƙarshen wannan kakar

Ɗan wasan mai shekara 35 da kwanaki wanda ƙungiyar ta ci tararsa, yana da matsayin wakilin buɗe ido na kasar Saudiyya.

Kocin PSG Christophe Galtie ya ce “babu abin da ya shafe shi” da dakatar da Messi, kuma ya yi Allah-wadai da zanga-zangar da magoya baya suka yi a ƙofar gidan Messi.

“Dakatarwar da aka yi wa Messi na da alaƙa da rashin ƙoƙarinsa a ƙungiyar, ba za mu boye komi ba.

“Babu abin da ya shafe ni da wannan hukunci. Ni ma labari aka ba ni. In nace na ji daɗi na yiƙarya.”

PSG ne ke matsayi na 1 da tazarar maki biyar da kuma wasanni biyar da ke gabansu, sai dai an cire su daga Champions Lig an kuma cire su daga kofin French.

An samu zanga-zangar magoya baya bayan rashin nasarar da PSG ta yi a hannub Lorient.

Sun taru a wajen gidan ɗan wasan gaban Brazil Nyemar a ranar Laraba suna ihu kan cewa sai ya bar ƙungiyar.

Tun bayan raunin da ya ji a idon sawunsa ɗan wasan mai shekara 31 yake jinya.

Wannan mataki na magoya bayan ya sanya hukumomin ƙungiyar ƙara yawan jami’an tsaro a gidan Messi da Nyemar da ɗan wasanta na tsakiya ɗan Italiya Marco Verratti da kuma Galtier, haka kuma an ƙara jami’an tsaron a filin atisayensu.

About the author

habibjs

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.