Menene Sirrin Lionel Messi

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Shekara 15 bayan ya soma buga wasa a Barcelona, Lionel Messi na ci gaba da jan zarensa. Hasalima an yi masa lakabi da bakon-haure.

Kusan rabin shekarunsa, Messi ya fafata da Porto a filin wasa na Nou Camp – kuma ya yi ta kafa tarihin da babu kamarsa.

Talla

Babu wanda ya taba ci wa Barcelona (566) kwallo kamarsa, sannan ya zura kwallo (392) a La Liga yayin da ya ci wa kasar Argentina kwallo (65), baya ga kasancewarsa dan kwallon duniya na Fifa sau biyar sannan ya dauki kofi a Barca sau 33.

Yanzu yana da shekara 31, kuma bai nuna alamar gajiyawa ba, Messi ya zura kwallo 14 a wasa 13 na dukkan gasar da aka buga a kakar wasa ta bana – sannan ya bi sahun manyan ‘yan wasan da suka fi zura kwallo a gasar La Liga inda yake cin kwallo daya a duk minti 87 – duk kuwa da cewa makonsa uku bai buga wasa ba saboda karyewar da ya yi a hannunsa.

Menene sirrinsa?

Talla

Marubuta labaran wasannin kwallon kafar Spain Andy West da Guillem Balague,wadanda dukkansu suka rubuta littattafai kan dan wasan na Argentine sun yi bayani kan daya daga cikin abubuwan da suka sanya dan wasan ke ci gaba da jan zarensa ranar Alhamis a shirin BBC Radio 5 live Football Daily podcast.

” Akwai wani zance da ake yi cewa shi bakon-haure ne. Don haka me ya sa yake yin nasara?”in ji West. “Dan wasan baya na Barcelona Gerard Pique ne kan gaba cikin masu yi masa wannan shagube.”

Balague ya kara da cewa: “A kan wannan batu na bakon-haure, na yi tsokaci a cikin littafin da na rubuta inda na ce akwai abubuwa 11 mutum zai yi idan yana so ya zama kamar Messi kuma hakan ne ya sa ya zama bako. Bako ne kawai zai iya yin su.

” Samun iyaye na gari da kuma kwallon kafa – iyayensa sun yi hijira zuwa Australia. Kana ganin zai iya yin bajintar da yake yi yanzu da a ce an haife shi a can? Ba na tsammani. Eh, a kasar Argentina zai iya yi. dole ka kasance mai kwarin gwiwa da buri da azama da rashin son kanka da shugabanci da zalaka da hikima da kuma kwayoyin halitta kafin ka yi sa’a game da al’amuranka.

“Idan ka hada dukkan wadannan abubuwa, to za ka zama Messi. Ba a samu zarata irin Messi da yawa ba saboda yana da matukar wahala mutum ya hada duk wadannan abubuwa shi kadai.

“Shi tamkar dutse ne da ke fadowa daga sama, babu wanda ya isa ya hana shi bingirowa kuma zai danne duk abin da ya samu a kan hanyarsa .”

Yaya Messi ke ci gaba da inganta kwallonsa?

Messi, wanda ya ci kwallo 219 a wasa 650 da ya buga wa Barcelona, ya yi wasa karkashin shugabancin manajoji shida a Nou Camp kuma yanzu shi ne kyaftin din kulob din bayan Andres Iniesta.

West ya ce: “Shi dan wasa ne da ke sauyawa domin ya dace da dukkan yanayi, ko sabbin manajoji ko sabbin abokan wasa, ko sabon wurin wasa kuma ina ganin hakan yana da matukar muhimmanci.

“Idan dan wasan da ya fi kowa iya kwallo a duniya zai yi hakan ina ganin ya kamata mu ma mu dauki irin wannan hanya. Sai da ya daina buga wasa a matsayi na tara inda ya zura kwallo 91 a shekara daya [2012] saboda hakan ba ya aiki.

“Kusan dukkan shekara biyu ko uku ana sauya masa matsayi ko kuma a hada shi da sabbin abokan wasa. Ba shi ne yake zaben abin da yake so ba. hakan ba ya cikin manyan abubuwan da ya tsara yi, sai dai kawai yana bin abin da aka ce ya yi ne.

“A lokacin da yake farko-farkon wasansa, yana buga wasa irin na gwanayen jujjuya kwallo – yana iya yin wasu takun – wato kamar samun kwallo sanna ya ruga a guje zuwa inda raga take.

“Ba ya amfani da kalmar nan ta harshen Spain ‘pauza’, wadda dan wasa kan tsaya sannan ya taka kwallo – yana sunkuyar da kansa ne. Sai dai idan ka duba za ka ga cikin shekaru da dama ya nakalci salo daban-daban na murza tamaula. Yana iya jujjuya kwallo sannan yana da ilimin mika ta ga abokan wasansa cikin sauri.

“Ko da yake ba shi da kazar-kzar na rugawa a guje ya wuce sauran ‘yan wasa zuwa tsakiyar fili kamar yadda yake lokacin da ya fafata da Getafe a 2007, amma dai har yanzu yana iya kutsawa cikin abokan hamayyarsa. Yanzu ya fi zama cikakken dan wasa kuma ina ganin zai ci gaba da yin hakan nan da shekaru da dama masu zuwa.”

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 54

Yaya za a bai wa Messi umarni?

Hakan na nuna irin tasirin da Messi ke da shi a Nou Camp, domin kuwa ko da manajansa Ernesto Valverde ya yi amanna cewa dan wasan ya fi shi sanin abin da ya kamata a yi.

Balague ya ce: “A yanzu dai, Messi ne maganin duk wata cuta. Ya fahimci kwallon kafa fiye da kowa.

” Dayadaga cikin abubuwan da Valverde ya gaya min shi ne Messi yana yin tsokaci a kan wasa ko da yana kan benchi. Ka dua wasan da suka fafata da Sevilla inda aka sanya shi a minti 30 na karshen wasa amma ya sauya yadda aka buga wasan.

“Valverde ya soma nuna wa Messi wasu abubuwa inda zai ce – ‘Ya kama ta ka sani Leo, cewa akwai bukatar ka yi… ka yi duk abin da kake so kawai.’

” Yakankalle shi sannan ya ce ‘wane irin bayani zan yi ga wannan yaron?'”

Mecece makomar Messi?

Messi yana hutu daga buga wa Argentina wasa, bayan da ya gaza ci yo mata wani babban kofi, inda ya sha kaye a wasannin karshe hudu. Kwantaraginsa a Barcelona zai kare a 2021 kuma ya ce ba zai iya buga wa wani kulob wasa ba sai boyhood club Newell’s Old Boys .

West ya ce: “Labarin Messi yana shaida mana cewa rashin tunanin ne ka yi hasashen abin da zai yi nan gaba.

” An yi sauye-sauye ne kawai ba tare da son ransa ba. Bamu san irin sauyin da Barcelona zai yi ba. Idan dai Ousmane Dembele zai iya zama dan wasa mai muhimmanci dole ne Messi ya sauya yadda yake murza leda.”

Amma fa komai zai iya shan bamban

Mu kaddara cewa Lionel Messi yana jagorantar Como wajen yin nasara kan Barcelona a wasan karshe na gasar cin kofin Zakarun Turai.

A cewar dan jaridar wasannin kasar Italiya James Horncastle wasu za su ga tamkar hakan ba mai yiwuwa ba ne, amma fa komai zai iya zama daban ga Messi.

“Ya samu kulob din da ya dace da shi da yanayinsa da kuma iliminsa ta yadda zai murkushe ci gaba da ‘yan wasa ke samu,” in ji shi. “Dole ya rika sassauta wa ‘yan wasa a fagen wasa.

“Fabio Capello ya ba da labarin lokacin d Juventus suka buga wasa daBarcelona, inda ya ga Messi sannan ya ce: ‘Ina son sayen wancan dan wasan, ina so a ba ni aron sa’. Daga karshe, hakan bai yiwu ba.

“Shugaban Genoa ya yi ikirarin cewa ya gwada Messi lokacin da yake Como kuma da a ce Como sun saye shi da sun zama Zakarun Turai da na Duniya.

“Da ya zama wani abin sha’awa a gan shi yana wasa a karkashin shugabancin Capello kuma a gani ko hakan zai kawo wani sauyi.”

Zai yi wahala Messi ya buga gasar Firimiya a yanzu amma Balague ya kara da cewa: “Na tambayi Messi kan abin da jama’a a Ingili ke cewa: ‘Ba za ka iya buga tamaula da daddare a cikin yanayin sanyi ba a Stoke.’

“Ya ce: ‘Ya kamata su je su ga filin da na yi wasa a Rosario.'”

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: