Wasanni

Me Yasa Har Yanzu Messi Bai Saka Hannu A Barcelona Ba?

advertisement

A satin daya gabata ne kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tab akin shugaban kungiyar, Joan Laporta, ta tabbatar da cewa dan wasan kungiyar Lionel Messi ya amince zai ci gaba da zama a kungiyar zuwa karshen kakar wasa ta shekarar 2026, sannan zai kuma karbi rabin albashin da kungiyar take biyansa wato ya rage kashi 50 cikin dari.

Sai dai Messi mai shekara 34 a duniya, wanda rahotanni ke cewar yana karbar albashin fam miliyan 123, kuma wanda yarjejeniyarsa ta kare a Barcelona ranar 30 ga watan Yuni bai saka hannu ba a hukumance duk da cewa ya amince da ci gaba da zaman.

Messi dai yanzu yana hutu, bayan da Argentina ta lashe gasar Copa America, kuma ba a fayyace kunshin yarjejeniyarba sai dai sake ci gaba da buga wasa da Messi zai yi yana daga cikin alkawarin da sabon shugaban Barcelona Joan Laporta ya yiwa magoya bayan kungiyar a lokacin da yake neman su sake zabensa a karo na biyu.

Tuni a watannin baya aka dinga alakanta Messi da cewar zai koma kungiyoyin Paris St-Germain ta kasar Farana ko kuma kungiyar Manchester City ta Ingila domin ci gaba da wasa tare da Pep Guardiola.

Sannan an kuma ta cewar kyaftin din na Barcelona, wanda ya lashe kofuna da dama a kungiyar zai koma buga gasar kwallon kafar kasar Amurka kamar yadda wasu daga cikin ‘yan wasa sukeyi idan suka fara girma.

Tauraron na Argentina dai shi ne a kan gaba wajen zura kwallaye a Barcelona saboda kawo yanzu yana da kwallaye 672 a raga, wanda ya lashe La Liga 10 da Champions League hudu haka kuma ya ci gasar Copa del Reys guda bakwai da lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Fifa na duniya karo shida jumulla.

Sai dai har yanzu Barcelona na kokarin yin musaya da dan wasanta, Antoine Griezmann, ita kuma ta karbi dan wasan Atletico Madrid, Saul Niguez, da nufin rage albashin da Griezmann din yake karba a duk shekara.

Daman dai tun kafin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da wannan labarin jaridun Banguardia da kuma ESPN suka bayar da rahoton cewar Messi na daf da sa hannun kan yarjejeniyar da rage albashi.

Laporta dai yana kokarin rage albashin da kungiyar take bayarwa tun lokacin da ya karbi shugabancin Barcelona, kuma yana bin ‘yan wasa da rarrashi domin rage albashin saboda bin ka’idar kashe kudi kamar yadda hukumar La Liga ta gindaya

Lokacin hirarsa da manema labarai, shugaban hukumar kula da gasar La Liga, Jabier Tebas ya bayyana cewa ba za su yi wa kungiyar Barcelona sassauci ba, wadda bashin da ke kanta ya kai Yuro biliyan daya kawo yanzu.

Idan baku manta ba a shekarar 2017, Messi ya saka hannu kan ci gaba da buga wasa a kungiyar Barcelona kuma mafi tsoka a duniya, in ji wani rahoto da jaridar El Mundo ta wallafa a watan Janairun wannan shekarar.

Kociyan Barcelona, Roland Koeman dai ya na son gina kungiyar da fitattun ‘yan wasa domin tunkarar kakar da za a fara ta shekarar 2021 zuwa 2022, inda ta sayar da wasu daga cikin ‘yan wasanta kamar Junior Firpo da Jean-Clair Todibo da kuma Carles Alena.

Sannan hakan ne ya bai wa kungiyar damar daukar tsohon dan wasan Manchester City, Sergio Aguero da dan wasa Memphis Depay da kuma Eric Garcia, matashin dan wasa wanda shima ya koma kungiyar a kyauta.

A ranar 10 ga wannan watan ne Messi mai shekara 34, ya lashe gasar cin kofin Copa America kuma a karon farko a babbar tawagar Argentina tun shekarar 1996 inda suka ci Copa America, bayan doke Brazil mai masaukin baki.

Bayan dai kammala gasar, Messi ne ya lashe kyautar dan wasan da ya taka rawar gani a Copa America tare da dan wasa Neymar, kuma shine kan gaba a cin kwallaye saboda yana da kwallaye hudu a raga, kuma shi ne wanda ya fi bayar wa a zura kwallo a raga a gasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button