Labarai

Me Ya Sa Tinubu Ke Ta Ziyarce-ziyarce A Jihohin Arewa?

Daga Comr Abba Sani Pantami
Ahmed Bola Tinubu, ya isa jihar Kano duk da adawar da ake nunawa kan gudanar da bikin ranar haihuwarsa a jihar.

Kungiyar tuntuba ta matasan Arewa (AYCF) ta nemi Gwamna Abdullahi Ganduje da kar ya karbi bakuncin gudanar da bikin ranar haihuwar ta Tinubu a jihar.

Amma a ranar Lahadi, Ganduje ya raka jigon Jam’iyyar ta APC zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Kano, inda ya yi masa mubaya’a.

A yau Litinin ne ake sa ran Tinubu zai gana da Majalisar Sarakunan Gargajiyan Nijeriya.

Akwai alamu da ke nuna cewa Tinubu ya zura wa kujerar shugaban kasa ido, duk da cewa bai fito fili ya bayyana aniyarsa ba.

Amma hakan ya fara tabbata idan yadda a kwanakin nan yake ta ziyarce ziyarce a wasu daga cikin manyan yankunan Arewa, zuwa yanzu yakai ziyara a Jihohin Sokoto, Katsina, Kaduna yanzu yana jihar Kano, bayan jihar ta Kano ana ta rade radin zai cigaba da ziyarce ziyarce zuwa wasu Jihohi.

Alamu karara sun fara tabbata ziyarar yawan fara kaddamar da neman shugabancin Nijeriya ya fara, wanda tuni yan Arewa da dama suka fara bore tare da maganganu marassa dadi.

Idan al’umma da dama suke aibanta shi kan halin ko’in kula da ya nuna a lokacin da ‘yan kudancin kasar suke kashe yan Arewa a rikice rikecen da suka fara a kwanakin baya, wanda yin shirun da yayi baice komai ba kan kisan da aka dinga yiwa ‘yan Arewa mazauna yankin kudancin Kasar, hakan ya tunzura Al’ummar Arewa.

Inda da dama daga cikin al’ummar yankin Arewa suke ta tofin Ala tsine akanshi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: