A kowacce shekara miliyoyin musulmai suna azumi tun daga fitowar rana har faduwarta, na tsawon kwanaki 20 ko 30 a cikin watan Ramadan.
A shekarun baya-bayan nan dai Ramadan na fadowa ne a watannin bazara a kusurwar duniya daga arewa, hakan zai janyo ranaku masu tsawo da kuma yanayi mai dumi.
Hakan na nufin cewa wasu kasashe kamar su Norway, mutane za su yi azumi na tsawon sa’o’i 20 a wannan shekarar.
Shin yin azumi zai iya yi wa jikin mutum illa? Ga abin da ke faruwa da jikinku idan kuka yi azumi na tsawon kwanaki 30.Lokaci mafi wuya – kwanaki biyu na farkon azumi
A ka’ida dai jikin mutum ba ya shiga yanayin azumi sosai sai an shafe sa’a takwas bayan abinci na karshe da mutum ya ci.
Wannan shi ne lokacin da cikin mutum ya gama narkar da abubuwan gina jiki da ya samu daga abincin.
Jim kadan bayan wannan lokacin, jikinmu zai koma wa sikarin da ke adane a hanta da tsokar jikinmu domin samun karfi.
Bayan dan lokaci kadan, idan sikarin ya kare, to kitse ne zai koma wuri na gaba da jiki zai iya samun karfi daga gare shi.Idan jikin mutum ya fara kone kitse, wannan na taimakawa wajen rage kiba da rage maiko da kuma rage yiwuwar mutum ya kamu da ciwon siga.
Amma, raguwar yawan sikarin da ke jikin mutum zai iya janyo kasala da rashin karfi.
Za ku iya fuskantar ciwon kai, da jiri, har ma da tashin zuciya da warin baki.
A wannan lokacin ne mutum ke fuskantar tsananin yunwa.
Hattara da rashin ruwa a jiki – Rana ta 3 zuwa ta 7
A lokacin da jikin mutum ya fara sabawa da azumi, kitse na raguwa kuma shi ne ke zama sikari a jini.
Dole sai an mayar da ruwan da mutum duk ke rasawa a yayin azumi, in ba haka ba zufa za ta iya janyo rashin ruwa a jiki.
Shan ruwa yana da amfani idan mutum yana azumi musamman ma a watannin bazara
Dole ne abincin da mutum zai ci ya kasance masu gina jiki da masu kitse.
Yana da muhimmanci mutum ya samu abinci mai gina jiki, wanda ke da gishiri da ruwa.
Sabawa da azumi a yanzu – Rana ta 8 zuwa ta 15
A mataki na uku, ya kamata mutum ya fara ganin sauyi a yanayinsa a yayin da jiki ya fara sabawa da azumin.
Dr Razeen Mahroof, wani kwarare kan maganin da ke kashe ciwo da bangaren kulawa ta musamman a asibitin Addenbrooke’s da ke Cambridge, ya ce baya ga haka azumi na da amfani daban-daban.
Azumi na taimakawa jiki wajen samun sauki cikin gaggawa da kuma hana jiki yaki da cututtuka
”A rayuwar mu ta yau da kullum ba kasaifai ake cin nau’ikan abinci daban-daban ba, kuma hakan na hana jiki gudanar da ayyukansa yadda ya kamata”
”Ana gyaran hakan a lokacin azumi, yana karkatar da jiki ya yi aikinsa da ya kamata.”
Azumi na taimakawa jiki wajen samun sauki cikin gaggawa da kuma hana jiki yaki da cututtuka.
Tsaftace ciki – Rana ta 16 zuwa ta 30
Idan aka ci rabin watan Ramadan, jikin mutum yana sabawa da azumi.
Hanji da koda da huhu da ma fatar mutum na tsaftace kansu.
Dr Razeen Mahroof ya ce azumi na taimakawa wajen rage kiba
”A wannan mataki, wadanan sassa na jiki sun dawo da aiki yadda ya kamata. Kwakwalwar mutum da hankalinsa na sauyawa kuma ana samu karin kuzari,” in ji Dokta Mahroof.
”Jikin mutum na kasa samun karfi. Wannan shi ne lokacin da yake shiga cikin ‘yunwa’ kuma ya kan samu kuzari. Hakan na faruwa ne idan mutum ya tsawaita azumi zuwa kwanaki da makonni.”
”Ayayin da ake azumtar Ramadan daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana, muna da damar tsara jiki ya samu abinci mai gina jiki da wadataccen ruwa. Hakan na gyara jiki da kuma taimakawa wajen rage kiba.”
Shin azumi na taimakawa Lafiyarmu?
Dokta Mahroof ya ce eh, sai dai ya gindaya sharudda.
”Azumi na da kyau ga lafiyarmu saboda yana taimakawa wajen mayar da hankali kan abin da za mu ci da kuma lokacin cin su.
Sai dai kuma, duk da cewa babu matsala idan mutum ya shafe wata yana azumi, ba shawara ba ce a kuma zarce da azumin ba.”
Azumin Ramadan, na taimakawa jiki ya daidaita kansa, hakan na iya nufin rage kiba da narkewar kitse marasa amfani
”Ci gaba da azumi ba hanya mai kyau ba ce na samun raguwar kiba na tsawon lokaci saboda sannu a hankali jikinka zai daina narkar da kitse don kara ma kuzari, kuma za ka tara kwanji.
Hakan matsala ce ga lafiya domin yana nufin jikinka ya shiga yanayi na yunwa’.”
Likitan ya shawarci cewa ban da watan Ramadan akwai lokutan da mutum ka iya ware a sauran watanni ko mu ce kwanaki a cikin sati da mutum zai iya azumi – misali sau biyu a sati – hakan ya fi taimakawa lafiya.
”Azumin Ramadan, na taimakawa jiki ya daidaita kansa, hakan na iya nufin rage kiba da narkewar kitse marasa amfani.”
Add Comment