Mayakan Boko Sun Sake Kai Hari Kan Sansanin Soja

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta AFP ta bayyana a jiya Juma’a, wannan hari ya auku bayan kwana guda da taron shugabannin kasashe biyar na nahiyyar Afirka inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a kasar Chadi.

Ganawar shugabannin kasashen ta gudana ne domin tattauna batutuwa da tsare-tsare gami da manufofin kawo gami neman goyon bayan kasashen duniya wajen karshen kungiyar ta’adda ta Boko Haram da a halin yanzu tsagerancinta ke ci gaba da habaka.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
Talla

‘Yan Shi’a Sunyi Fito-Na-Fito da Jami’an…

1 of 661

Harin ya auku ne yayin da mayakan suka ribaci manyan makamai na kare dangi wajen zartar da ta’addanci a sansanin dakarun soji da ke kauyen Arege daura da cibiyar sana’ar Su ta garin Baga a gabar tafkin Chadi.

Rai daya ya salwanta, Mutane 7 sun jikkata a wani sabon Harin Boko Haram kan Dakarun Sojin Kasa Majiyar rahoton ta AFP ta bayyana cewa, harin na bazata gami da kwanton bauna ya auku da sanyin Asubahi kamar yadda wani jami’in soji da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayanna.

Rahotanni sun bayyana cewa, dakarun sojin cikin tsayuwar daka ta jiran tsammani da ko ta kwana sun samu nasarar mayar da martani tare da dakile wannan hari da a yayin haka rayuwar daya daga cikin su ta salwanta baya ga jikkatar kimanin dakaru bakwai a filin daga.

#Rariya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: