Nasiha

MATSALOLIN SAKIN AURE BANGAREN MAZA


MATSALOLIN SAKIN AURE BANGAREN MAZA
Akwai matsalolin maza da yawa wanda yake
haddasa rashin zaman lafiya a cikin aure ko
kuma saki. Sune kamar haka: –
1. Karya
2. Rashin kulawa da rashin tsafta
3. Cin amana
4. Zargi
5. Matsalar iyaye
6. Matsalar yan’ uwa
7. Matsalar abokai
KARYA:
wasu mazan suna yiwa matayen da zasu aura
karya ta hanyar nuna masu cewa sun mallaki
wani abun duniya wanda a zahiri kuma babu
abin, ita kuma matar zata soka tareda kwadayin
samun wannan abun, bayan anyi aure, idan
macen taje gidan mijin kuma tasami akasin
abinda yake fada mata to dole zasu samu
matsala wanda daga karshe dole zatace ya
saketa ko kuma su zauna cikin matsala kullum.
RASHIN KULAWA
Da yawa daga cikin maza na Hausa/Fulani basa
kulawa da matansu, wanda ita kuma mace babu
abinda takeso samada kulawa, idan har ya zama
baka iya kulawa da bukatar matarka kamar
abinda ya shafi abinci, sutura da dukkanin
sauran bukatunta, to dole zasu sami matsala da
mijinta wanda zai iya kawo rabuwarsu.
Kulawa ta biyu kuwa itace, duk mace tanason
ace mijinta yana bata lokacinta wajen debe mata
kewa, zama da ita domin jin ra’ayinta da kuma
bukatunta, sannan kuma ka tabbatar mata cewa
lallai kana sonta wanda hakan shima yayi
karanci a cikin maza. Wannan matsalace babba
wanda rashin samun hakan yana kawo matsala
sosai har akaiga rabuwa.
RASHIN TSAFTA
Duk mace tanason taga mijinta yanada tsafta da
kuma kula da jikinshi, kamar yanda namiji
yakeso yaga matarshi da tsafta kullum haka
itama takeso amma zaka samu cewa hausawa
da yawa basuda tsafta, wasu kuma suna da ita
amma basuyi sai zasu fita kasuwa ko aiki, badai
a cikin gidansu ba, basuyi don matansu wanda
wannan shima yana kawo matsala ko kuma
rabuwa.
CIN AMANA:
Dayawa daga cikin maza sunacin amanar
matansu ta hanyar neman matan banza wanda
wasu lokutan sai kasamu cewa mace takama
mijinta da matar banza ko a cikin gidanta ko
kuma a waje wanda wannan yana kawo
rabuwar aure.
ZARGI: Maza dayawa sukanyi zargin matansu
akan abinda ya zamanto su matan basa
Aikatawa. 
Haiman Khan Raees 
@HaimanRaees

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.